Jiragen Yaƙi A-Super Tucano Sun Iso Najeriya

  • Home
  • Labarai
  • Jiragen Yaƙi A-Super Tucano Sun Iso Najeriya

Rukunin farko na jiragen yaƙi A-29 Super Tucano da ake tsimayen isowarsu Najeriya sun iso. Ana sa ran ƙaddamar da su ga rundunar sojin sama a watan Agusta.

Jaridar HumAngle ta ruwaito cewa kashin farko na jiragen guda shida, wanda wani jirgi ya yi wa rakiya sun iso filin jirgin sama na Kano a ranar 22 ga Yuli, 2021.

Jirgin dake tafe da su (Dornier Do-328-110) ya sauka ne a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da misalin ƙarfe 12:50 na ranar Alhamis, wanda ya taso daga ƙasar Algeria, inda ya yada zango a ranar Laraba.

A sanarwar da rundunar sojin saman Najeriya ta fitar a baya, jiragen za su baro Amurka sannan su yada zango a Canada da Greeland da Iceland da Spain sai Algeria, inda daga nan ne za su ƙaraso Najeriya.

Kamfanin tsaro na Embraer ya tabbatar da cewa jirgin A-29 Super Tucano ya ci kuɗinsa saboda cigaban da yake da shi ta fuskar kai hari, da kai agaji tare da naɗar bayanan sirri da sauransu.

A shekarar 2018 ne rundunar sojojin sama ta Najeriya ta bawa kamfanin tsaro na Embraer Defense & Security da Sierra Nevada Corporation kwangilar ƙerawa da kawo jiragen Super Tucano guda 12 ƙasar.

Bayan tabbatuwar kwangilar, gwamnatin Najeriya ta biya kuɗin jiragen tare da hidimarsu daga kuɗi na musamman da ake warewa don tsaro daga asusun rarar ɗanyen mai.

Za a yi wa waɗannan jirage matsugunni ne a Kainji dake jihar Niger, inda aka gina waje na musamman da duk na’urorin kai ɗauki na kuɗi dalar Amurka miliyan 36.1 da aka bawa rundunar sojin Amurka (United States Army Corps of Engineers) kwangilar aikin.

Tags:
%d bloggers like this: