Ahmad Musa Ya Kammala Sauya Sheƙa Zuwa Ƙungiyar Fatih Karagumuk

  • Home
  • Wasanni
  • Ahmad Musa Ya Kammala Sauya Sheƙa Zuwa Ƙungiyar Fatih Karagumuk

Ƙungiyar kwallon ƙafa ta ajin manya na Super Lig a ƙasar Turkiya, Fatih Karangumuk sun kammala cike-ciken tabbatar da kwantaraginsu da Ahmad Musa.

Ƙungiyar da ba ta taɓa lashe wata babbar gasa ba ta yi nasarar samun kaftin ɗin Super Eagles, bayan rushe kwantaraginsa da Kano Pillars da aka yi bisa wannan yarjejeniya a baya.

“Mun samu ƙarawuwar ɗan wasan gaban Najeriya mai shekaru 28 a cikin tawagarmu” A wata sanarwa da ƙungiyar kwallon kafar ta fitar.

“Muna yi wa Ahmad Musa fatan nasara a cikin rigar Karagümrük, wanda mataimakin shugabanmu, Serkan ya rattabawa hannu tare da Daraktan wasanni, Murat Akın.”

Tags:
%d bloggers like this: