Wasu Mayaƙan Boko Haram Da Na ISWAP Sun Miƙa Wuya

  • Home
  • Labarai
  • Wasu Mayaƙan Boko Haram Da Na ISWAP Sun Miƙa Wuya

Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da labarin wasu mayaƙan Boko Haram da na ISWAP su 28 tare da iyalansu sun miƙa kansu ga dakarun rundunar bataliya ta 151 a jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar sojin, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya sanar da haka a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce mayaƙan sun tsere ne daga sansaninsu, sakamakon hare-haren sama da ake kai musu. A yanzu waɗannan mayaƙa sun miƙa wuya ga dakarun bayan da suka fuskanci ba za su kai labari ba.

“Cikin su akwai maza 11 da mata biyar da ‘ya’yansu 12. Sannan mun samu jigidar harsasai 27 da AK47 uku da sauran makamai,” in ji sanarwar.

Tags:
%d bloggers like this: