Yadda Aka Harbo Jirgin Yaƙin Najeriya: Me Hakan Yake Nufi Ta Fuskar Ƙimar Ƙasar

  • Home
  • Tsokaci
  • Yadda Aka Harbo Jirgin Yaƙin Najeriya: Me Hakan Yake Nufi Ta Fuskar Ƙimar Ƙasar

Rundunar sojojin saman Najeriya ta tabbatarkuɓutar sojanta, wanda ‘yan bindiga suka harbo jirgin da yake ciki a lokacin da yake dawo wa daga wani farmaki a yankin Zamfara. Abin farin ciki ne yadda sojan ya kuɓuta, sannan a lokaci guda abin baƙin ciki ne yadda ƙasar ta yi asarar jirgin yaƙi.

An ce sojan ya yi amfani da lemar saukowa daga jirgi lokacin da ya tabbata jirgin faɗowa zai yi. Duk da haka ‘yan ta’addan sun yi ƙoƙarin cimmasa, amma ya tsare tare da fakewa a wani ƙauye. Ya yi amfani da wayarsa a kashegari, inda ya samu kuɓuta tare da danganewa da wani sansanin sojojin Najeriya.

Amma ni abin da ya fi damuna shi ne yadda aka harbo wannan jirgin. Dama haka abin yake, jirgin yaƙi kamar na fasinja yake, ba shi da wata kau dabara ko waskiya?

Daga shekarar da ta gaba zuwa yau an harharbo jiragen Najeriya a yayin artabu da ‘yan ta’adda.


Haka za a dinga wannan asara duk da uban kuɗin da ake kashewa wajen sayansu? Ko kuma jiragen ba su iya layar zana ba ne, ko kuma matuƙan ne ba su da kwarewa, ko kuma in ce muna amfani da jiragen da yanzu ba a yayinsu?

A yanzu haka wasu samfurin jiragen yaƙi na zamani ƙirar Super Tucuno sun baro ƙasar Amurka, suna kan hanyarsu ta zuwa Najeriya. Ana sa ran zuwansu karshen wannan wata da muke ciki.


An yi itifakin jirage ne masu matuƙar hatsari, wanda sai da aka sha tababa wajen sayensu, musamman yadda ƙasar Amurka ta dinga jan ƙafa a yarjejeniyar kasuwancin jirage. A ƙarshe dai kashin farko na jiragen guda shida na kan hanya, bayan da Amurka ta horar da sojojin Najeriya a kan sarrafa su.
Maganar da nake son zuwa kanta ita ce, haka shi ma Tucuno za a dinga harbo mana shi, kamar yadda ake ɓarin gyaɗa. Ko shi wannan jirgin irin mai walƙiya ne da muke jin labari?
Yawan kakkaɓo jiragen yaƙin Najeriya na nuna gazawa. Su kansu ‘yan ta’adda na ganin tsinkensu ya kai tsaiko. Hakan ya sa raini kan ƙaru tsakanin sojojin da ‘yan ta’adda. Irin wannan raini ne yake sa ‘yan bindiga kan tunkari sansanin sojojin Najeriya gaba gaɗi.Wannan ba ƙaramin zubar da mutuncin ƙasar ya yi a idon duniya ba.

Ko ma ya ya abin yake sai Najeriya ta yi aiki da ƙa’ida wajen gudanar da jiragen yaƙinta. Na farko dai, dole jiragen su samu kulawa sosai na dangane gyaransu kamar yadda aka tsara musu. Na biyu dole a cigaba da kashe kuɗi wajen bada horo. Sanin makamar aiki a kowanne ɓangare shi ne tushen nasara. Sai uwa uba walwalar mayaƙan. Ai dama harkar tsaro na da kaso mai tsoka a kasafin kuɗi, wanda idan aka yi amfani da shi ta hanyar da ya kamata za a ga cigaba.

Duniya ta cigaba ta fannin yaƙi daga sama, tun daga jiragen zamani zuwa jiragen da basu da matuƙi. Idan Najeriya ta yi ƙoƙarin inganta wannan ɓangare za a ga sauyi sosai. Allah ya ɗora Najeriya a kan maƙiyanta.
Zadeen Kano

Tags:
%d bloggers like this: