ILMIN MATA

Daga

Rukayya Muhammad Maikarfi

Rabbi Ubangiji gwani mahaliccina,

ka yi min lamuni in bude bakina,

in zuba baituka da fatar bakina,

in fadakarwa a kan ‘yancin mata.

Kayyi dubun salatika ga ma’aikina,

da ya zam sannadi ga samun ‘yancina,

wancan lokaci muna a cikin kuna,

da zuwan Musdafa mukaz zama ‘yan gata.

Da in anka haifi jinsiyyar mata,

al’ada ta Larabawa manufata,

haka rami suke su binne ‘yan mata,

da zuwan Musdafa mu kai ‘yanci mata.

Ko ka gano miji da mata zancen da,

sun yanke mu’amala don al’ada,

ba shi bidar ya gan ta ko ya yi tawaida,

da zuwan mursali a yau mun inganta.

Addini ya ba mu ‘yanci mu mata,

mu yi ilimi mu kau da jahilci mata,

“dalabul ilmi” babu inda ya fifita,

jinsin ‘yan maza da mata manufata.

Amma yau a rayuwa an bambanta,

an yi mana ka’ida fa ta ilimanta,

wai an ware ilimin da ya cancanta,

mu mata mu san shi don ba mu da gata!

Ku yi nazari a bangaren addini na,

mace da tai izu guda kujji batuna,

ka ji ana fadin ta sami lumana,

a gidan aurenta ta sami na bauta.

Ilimin zamani ko ba a son mata,

su yi azama su san shi wai sun shiga bata,

mamaki ya kan saka ni in dokanta,

za a yi haihuwa ana neman likita.

Sunana Rukayya mai kishin mata,

Allah Rabbana ka daukaka manufata,

A zukatan mutan gari fa su ilmanta,

Su yi katari su kau da jahilcin mata.


Kafin rasuwarta, Rukayya Muhammad Maikarfi, ta kasance daga cikin marubutan da ke da baiwar yin rubutu cikin harshen Hausa da Turanci. Ta bada gudunmawa sosai a harkar adabi, musamman a kungiyarta ta marubuta ta ANA Kano. Allah ya yi mata rasuwa sanadiyar hadarin mota. Ta rasu ta bar mijinta da ‘ya’ya hudu. Allah ya ji kanta ya sa Aljanna makoma.

Tags:
%d bloggers like this: