Ahmed Musa Zai Koma Buga Wasa A Turkey

Ɗan wasan ƙungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Ahmad Musa na shirin barin ƙungiyar don komawa ƙasar Turkey, inda zai fafata a gasar Super Lig ta ƙasar. A kwantaragin shekara ɗaya da ya sanya wa hannu, ɗan wasan zai karɓi kuɗi €2.2 miliyan (naira biliyan 1.05). Ana sa ran tafiyarsa ƙasar Turkey a sati mai kamawa.

Hakan ya fito daga bakin dillalinsa, Justus, wanda ke zaune a Amurka. Sai dai bai faɗi wacce ƙungiya ce ta ɗauki fitatcen ɗan wasan ba. “Da farko ƙungiyar kwallon sun yi wa Musan tayin €2 miliyan a tsawon shekara, amma bai karɓa ba.”

“Shugaban ƙungiyar ya ce ba za su iya bada sama da hakan ba, saboda matsalar kuɗi da ƙungiyoyi ke fama da ita a ƙasashen Turai a dalilin annobar korona.”

“Amma, shugaban ƙungiyar ya ce sun ɗokanta su ga Musa a cikin jerin waɗanda suke biya a kakar wasa mai zuwa, hakan ya sa suka sake bada tayin ƙarshe na €2.2 miliyan a shekara,” a cewarsa.

Ga rahotanin da muka samu, Ahmad Musa mai shekara 28 ya amince da tayin da suka yi masa kuma zai garzaya can Turan don ya rattaba hannu a kwantaragin a sati mai kamawa.

A 13 ga watan Afrilu ne kafin ɗin Super Eagles, Ahmad Musa ya dawo tsohuwar ƙungiyarsa ta Kano Pillars don ƙarƙare gasar rukunin kwararru ta Najeriya (Nigerian Professional Football League (NPFL) season) ta wannan shekara.

Dama a yarjejeniyar da ya sawa hannu da ƙungiyar Kano Pillars ita ce koyaushe ya samu wata ƙungiya a ƙasashen ƙetare za su sake shi.

Tags:
%d bloggers like this: