ƊAN BILKI KWAMANDA KA KULA DA HARSHENKA KWAMANDA YA YI MAKA NISA FIYE DA SAU MILIYAN BA ADADI

  • Home
  • Siyasa da Shugabanci
  • ƊAN BILKI KWAMANDA KA KULA DA HARSHENKA KWAMANDA YA YI MAKA NISA FIYE DA SAU MILIYAN BA ADADI

DAGA Shariff Aminu Ahlan

Duk mai bibiyar kafafen sadarwa na yanar gizo da gidajen rediyo ya na sane da maganganun rashin hankali na dagajin ɗan siyasa marar lissafi da ƙwarewa, karuwar siyasa marar tsari, wanda ake kira da Ɗan Bilki Kwamanda.

Sunansa ya na nan tsawon shekaru ya na ta’ammuli da ruɗu da maganganun rashin daraja da rashin kan gado da rikici da rigingimu da jita-jita da ƙarya da ƙazafi da kitsa sheɗanci da haddasa husuma da kasuwanci da cinikayyar mabiyansa na siyasa marasa daraja a farashin da bai kai ya kawo ba saboda jahilcinsa na rashin ilimin addini da na boko.

A wannan fage na wasan siyasa wanda ya ke ɗauke da tsare-tsaren manufa da buruka a tsakanin ƴan siyasa, ya ƙirƙiri ƙarfafan haɗi na ƙarya sannan ya fara rera amonsa a babban tsauni da neman manyan kuɗaɗe ƙarƙashin ƙungiyarsa ta sadarwa marar rijista wacce ya kira da suna Arewa Media Forum ƙungiyar da babu wani wuri da za a nuna ace nan ne adireshinta ko kuma Ofishinta ko tsarinta na shugabanci. Ɗan siyasa marar tsari wanda ya ke kallon siyasa a matsayin ƙwarewar haɗa biredi da bota sannan a kowane lokaci a shirye ya ke, zumuɗi ya ke a matse ya ke ya rusa muhimman mutane idan har an cimma yarjejeniyar za a biya shi.

Abubuwan da ya yi a bayyane su ke an san su ya faro daga kan shugaban ƙasa, zuwa Dambazau sai Abdul’aziz Yari ya faɗo kan Baffa, One2Tell10 ɗaya ya faɗawa goma ya juya kan Ahmad Idris yanzu ya riƙe Sanata Barau Jibrin Maliya.

Babu wanda zai dakatar da kai daga sayar da cinikayyar ƴan takararka, bayan da komai na rayuwa lamari ne na zaɓin rai. Sai dai hanyar da kuma lafazin da ka ke amfani da su wajen sayar da ƴan takararka ya saɓa da kamala da girmamawa da kima da cikar hankali, da fiƙira da tausassan lafazin magana, sunayen da za a kira su shi ne shafa baƙin fenti da ruguza kima da ɓata suna da zarge-zarge da haddasa husuma saboda jahilcinka. Yanzu ka zunguro jelar damisa duk akan makauniyar manufarka ta ɗaukaka shugabanka wanda na yi imani ya na da cikar kamala ba zai yaba, ko ya goyi bayan wannan hargitsin siyasa ba.

Ka sanya a zuciyarka cewa Onarabul Murtala Sula Garo babban kwamanda, babban mayaƙi da duniya ta shaida ya yi maka nisa ta kowane fannin rayuwa fiye da sau miliyan ba adadi. A zumuɗinka na son faranta ran shugabanka da ya ke biyanka ka yi wauta zuwa ƙalubalantar ɗaya daga cikin membobi manyan masoya APC kana babban masoyi mai biyayya ga mai girma gwamna.

Babu wani ɗan siyasa a wannan lokaci da ya sha gaban Kwamanda ta fuskar kyautatawa da taimakon ƴaƴan jam’iyyar a duk faɗin wannan Jiha da kowane sashe. Muhimman mutane masu daraja kamar shugaban ma’aikata, Ali Makoɗa da Muhammad Garba da sauran wasu ƴan ƙalilan a kowane lokaci su na gwada aiwatar da halayya ɗaya wajen ba da tallafi da rage raɗaɗin damuwa ga miliyoyin mutane musamman ƴaƴan jam’iyyar APC.

Haka zalika, biyayyarsu ga mai girma gwamna a bayyane take ta gaskiya ce babu shakka balle kokwanto ko raba ɗaya biyu ko ƙalubale. A kowane lokaci mu na godiya a gare su, tare da amsa kiransu domin gaskiyarsu da adalcinsu sun cancanci haka. Ofishinsa a kowane lokaci kamar makka ya ke inda dubban mutane su ke gangamin zuwa neman alfarma ko wani abu mai kama da haka. Mai bayarwa a kowane lokaci ƙwararre wajen samar da sulhu da daidaito wanda cikin nasara ya tunkari waɗanda ba za su lissafu ba ya shiryawa samo mafita sannan kuma daga ƙarshe ya bunne ta da zaman lafiya wajen riƙe jam’iyyar da samar da ƙarfinta da biyayya ga mai girma gwamna.

Ka kalleta a matsayin gaskiya tsirararta wacce za ka bayyana ko ka ɓoye ta da kanka cewa zuwan mai girma gwamna ofis a karo na biyu za a girmama shi da tarihin da ya kafa da aikinsa na sadaukarwa ya yin da ƙwararru kan ha’incin zaɓe Kwankwasiyya su ka rufe kusa da sace hanyar hankali ta shugabanci. Babu buƙatar fito da abin da ya faru gaba ɗaya, komai ya na rubuce a ajiye.

Bari na nemi Ɗan Bilki da ya tunkari wata akuyar ya ƙalubalance ta, amma zai fi masa kyau ya gujewa shiga ramin Zaki. Har zuwa yau Kwamanda bai bayyana wani ƙudirinsa na neman wani matsayi na siyasa nan gaba ba. Sai dai ya maida hankali akan yadda zai ciyar da jam’iyyarsa gaba ta zama mai ƙarfi a zaɓe mai zuwa. Ɗan Bilki ya zama lallai ya kiyaye ya fahimci gaskiya ya san cewa miliyoyin mutane ciki har da ni za mu sanya shi kuka a fannin siyasa idan har ya cigaba da ambato sunan Kwamanda a karuwar kasuwancin siyasarsa.

Bai sanni ba saboda shi ba mai cikakken ilimi ba ne da zai iya karanta rubuce-rubucena na siyasa a shafukan jaridu ko yanar gizo ba. A matsayin da su ke kiran kansu na sojojin ba waɗanda su ke shiga kafafen sadarwa su bayyana ra’ayinsu na siyasa, mu za mu iya haɗa hanyoyi biyu a matsayin marubutan siyasa a jaridu da yanar gizo sannan kuma mu yi maganganu a gidajen rediyo da yare guda ta hanyar da za su fahimta yadda ya kamata. An haife mu mun kuma taso a matsayin Hausa Fulani wanda mu ke iya cikakkiyar magana da Harshen cikin murya mai ƙarfi da gamsarwa. Saboda haka, muryarku ko ma duk abin da su ke kiranku, ku fita daga hanyar Kwamanda ko kuma tarihinku ya shafe a siyasa.

Shariff Aminu Ahlan (Babban mayaƙi na gwamna Ganduje).

Tags:
%d bloggers like this: