Yan Bindiga Sun Kashe Manjo Janar Na Sojojin Najeriya

  • Home
  • Labarai
  • Yan Bindiga Sun Kashe Manjo Janar Na Sojojin Najeriya

Cikin alhini rundunar sojojin Najeriya ta sanar da rasuwar daya daga cikin manyan hafsoshinta, Manjo Janar Hassan Ahmed sakamakon wani harin da wasu yan bindiga suka kai masa a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja.

Wannan sanarwar ta fito daga bakin Daraktan yada labaran rundunar, Janar Onyema Nwachukwu, wanda ya rabawa manema labarai. Ya ce yan bindiga sun budewa motar Janar Ahmed wuta a daren jiya, abin da ya yi sanadiyar rasuwarsa.

Nwachukwu ya sanar da cewar shugaban rundunar sojojin, Laftanar Janar Faruk Yahya tare da sojojin ƙasar sun bayyana takaicin su da rashin Janar Ahmed wanda ake saran yi wa jana’iza a yau Juma’a, a makabartar sojoji dake Lungi a Abuja.

Tags:
%d bloggers like this: