Marubutanmu: Tare da Ado Ahmad Gidan Dabino, MON

  • Home
  • Adabi
  • Marubutanmu: Tare da Ado Ahmad Gidan Dabino, MON

An haifi Ado Ahmad Gidan Dabino, MON a karamar hukumar Dawakin Kudu a shekar 1964 dake jihar Kano. Ya yi karatun allo a Zangon Barebari. Bai samy damar yin karatun boka sai da ya kai shekara ashirin, sannan ya fara zuwa makarantar ilimin manya ta masallaci, wacce aka fi sani da makarantar Baba Ladi (Allah ya ji kansa). Daga nan ya yi karatu a makarantar sandandare ta GSS Warure inda ya samu satifiket na SSCE a 1990.

Bayan nan ya yi kwas na shekara guda a kan karatun makafi da koyon aikin kafinta, A shekarar 2005 kuma ya sami Diploma a kan aikin sadarwa daga Jamiár Bayero ta Kano. Ado Ahmad na daya daga cikin fitattun marubutan Hausa na zamani kuma littafinsa mai suna ‘In da So da Kauna’ na daya daga cikin fitattun littattafan Hausa na kowane zamani.

Ya rike mukamai da dama a kungiyoyin marubuta, shi ne shugaban Kungiya Marubuta ta Raina Kama, sannan yana daga cikin wadanda suka kafa Kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA), reshen jihar Kano wanda a lokacin kafa ta ya rike mukamin Mataimakin Shugaba, Ma’aji kafin ya zama shugabanta a shekara 2006.

 Gidan Dabino ya taba zama Edita na FIM magazine kasancewar daya daga cikin wadanda suka kafata a 1999. Shi ne mawallafin Mumtaz kuma Shugaba/Daraktan Gudanawarwa na Gidan Dabino International Nigeria Limited, sannan shi ne shugaba/Daraktan Gudanarwa na sabuwar jaridar Ajami mai suna Tabarau. Ya gabatar da makalu a manyan tarrurruka na karawa juna sani a jami’oí daban daban na Nijeriya.  Jarumi ne a shirin finafinan Hausa, fitatcen marubuci kuma dan jarida.

A Shekarar 2014 shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya ba shi lambar girmamawa ta kasa MON, bisa gudunmawar da yake bayarwa.

Tags:
%d bloggers like this: