Jiragen Yajin Najeriya Kirar Tucano Suna Kan Hanya Zuwa Kasar

  • Home
  • Labarai
  • Jiragen Yajin Najeriya Kirar Tucano Suna Kan Hanya Zuwa Kasar

Rundunar sojojin saman Najeriya, NAF, ta tabbatar da cewa kashin farko na jiragen yakin super tucano (A-29 Super Tucano) guda shida da aka jima ana dakonsu a kasar sun kamo hanya zuwa Najeriya daga Amurka. Kakakin NAF ne ya sanar da haka a wani jawabi da ya fitar. A cewarsa jiragen za su biyo ta wasu kasashe biyar kafin isowar su.

 Kakakin rundunar dakarun sojin sama, NAF, Edward Gabkwet, ne ya sanar sa haka a wani jawabi da ya fitar ranar Alhamis a shafn sada zumunta na facebook. Ya ce jiragen sun baro ƙasar Amurka ranar Laraba, kuma ana tsammanin isowar su Najeriya a kowane lokaci.

Jiragen super tucano jirage ne masu matukar hatsari da ake sa ran za su taimakawa Najeriya wajen yaki da masu tada kayar baya. Saboda irin hadarin da jiragen suke da shi ne, kasar Amurka ta dinga jan kafa wajen sayar da wannan jirage ga Najeriya, har sai da ta bada cikakken horo ga wasu sojojin Najeriya da za su yi amfani da wadannan jirage.  

Tags:
%d bloggers like this: