An Gurfanar Da Abduljabbar A Gaban Kotun, Za A Kuma Cigaba Da Ƙargame Shi Har Ranar Shariah Ta Gaba

  • Home
  • Labarai
  • An Gurfanar Da Abduljabbar A Gaban Kotun, Za A Kuma Cigaba Da Ƙargame Shi Har Ranar Shariah Ta Gaba

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya fara fuskantar hukunci bisa batanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (SAW). Abduljabbar ya yi kalamai da dama da muninsu ya taɓa zuciyar muminai.
Hakan ne ya sa aka gurfanar da shi a kotu a yau Juma’a.


Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan. A cewarsa an kai ga wannan mataki ne bayan karɓar rahoton farko da kwamishinan shariah na jihar Kano ya yi daga hannu ‘yan sanda, wanda da shi ne ya gabatarwa alƙali.


An gurfanar da Abduljabbar ɗin ne a yau Juma’a 16 ga Yuli a gaban babbar kotun shariah (Upper Shari’a Court) dake ƙofar kudu, bisa jagoranci Alƙali Ibrahim Sarki Yola, inda aka karanto masa laifukansa.
Sanarwar ta ƙara da cewa an ɗage zaman kotun zuwa ranar 28 ga watan Yuli, amma malamin zai cigaba da zama a hannun jami’an tsaron ‘yan sanda har zuwa ranar Litinin, inda za a tasa ƙeyarsa zuwa gidan maza, kafin ranar da za a cigaba da shari’ar.

Tags:
%d bloggers like this: