Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya sake shigar da ƙarar Jaafar Jaafar a babbar kotun tarayya a Abuja

  • Home
  • Labarai
  • Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya sake shigar da ƙarar Jaafar Jaafar a babbar kotun tarayya a Abuja

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sake shigar da ƙarar mawallafin jaridun Daily Nigerian, Mallam Jaafar Jaafar a babbar kotun tarayya dake Abuja. Ya shigar da ƙarar ne bisa zargin bata masa suna da jaridar Daily Nigeria ta yi na wallafa wanii faifan bidiyo da ya nuno gwamnan yana karɓar dalar Amurka daga ‘yan kwangila.

Gwamnan Kano tun fitar wannan faifan bidiyo ya karyata faruwar haka. Amma wani abin mamaki shi ne, mako biyu baya gwamnan ta hannun lauyansa ya bayyana janye ƙarar da ya yi. A saboda haka ne kotu dake shari’ar a jihar Kano ta buƙaci Gwamnan ya biya Jaafar Jaafar diyyar naira dubu dari takwas (800,000) tare da jaridarsa, bisa bata masa lokaci da ya yi.

Tags:
%d bloggers like this: