YADDA NAJERIYA TA LALLASA KASAR ARGENTINA A WASAN KWALLON KWANDO

  • Home
  • Wasanni
  • YADDA NAJERIYA TA LALLASA KASAR ARGENTINA A WASAN KWALLON KWANDO

‘Yan wasan kwallon kwando na ajin manya na Najeriya, D’Tigers na cigaba da samun gagarumar nasara a shirye-shiryen da suke na wasan Olympics, 2020 da za a gudanar birnin Tokyo. ‘Yan wasan sun yi nasara a kan kasar Argentina dake kan mizani na 4, a wani wasa da aka yi na yin damara a Las Vegas, a ranar Litinin, inda suka lallasu da ci 94 da 71.

Zakarun na Afirka sun yi wannan nasara ne bayan da a wasansu na baya suka bawa kasar Amurka kashi, kasar da ake zuzutawa a duniya a fagen kwallon kwando.

Da farko kasar Argentina na gaban Najeriya a zangon farkon wasan da ci 19 da 17. D’Tigers sun samu karsashi a zango na biyu inda suka samu maki 26 da 14, wanda hakan ya basu karfin guiwa har zuwa hutun rabin lokaci, da aka tafi suna da 43 da 33, tazarar maki goma.

‘Yan wasan na D’Tigers sun cigaba da wuta a zango na uku inda suka bawa abokan karawarsu tazar maki 19, wato 74 da 55. Kungiyar ta Najeriya ta karkare zangon karshe da maki 97 da 71.

Najeriya dai na ajin B tare da kasashe da suka hada Australia da Italy da Germany, kuma za su fara wasansu na farko ne a ranar 25 ga Yuli da kasar Australia a babban filin Saitama.

Yanzu dai mai horar da ‘yan wasan Najeriya, Mike Brown zai yi fama da kalubalen fitar da ‘yan wasa 12 da za tafi da su Tokyo kafin 17 ga Yuli, musamman duba ga irin rawar da ‘yan wasan nasa suka taka.

Tags:
%d bloggers like this: