YADDA AKE TSOTSE ARZIƘIN AREWA

Daga Mukhtar Mudi Sipikin

Bankuna suna hada-hadar kuɗi da yawa, kama daga bayar da bashi zuwa “transfer” Wannan hada-hada da su ke yi na janyowa masu bankuna ribar biliyoyin kuɗaɗe.

Arewa da ke da jama’a kusan Miliyan 140 ba ta da babban banki ɗaya mallakin mutanenta, sai dai irin ƙanƙana irin “micro finance” ɗinnan

A kullum, aƙalla Ƴan Arewa miliyan 20 ne ke “transfer” kuɗi ta hannun bankuna mallakin ƴan kudu, duk “transfer” a yanzu Naira 20 ce.

20 × Miliyan 20= Miliyan 400. Wannan shi ne kuɗin da ƴan Arewa ke bawa ƴan kudu a kullum, zai ma iya fin haka. 400,000,000 × 29 (Wata ɗaya) ya kama 11,600,000,000. Biliyan Sha ɗaya da Miliyan 600 kenan. A shekara zai kama 11,600,000,000 × 12= 139,200,000,000. (Biliyan 139.200)

A duk shekara Arewa na bawa Kudu wannan kuɗin, wanda tsaf zai iya:

  1. Gina gidaje masu sauƙin da yawa a Arewa.

ko kuma

  1. Gina makarantu a ƙauyekanmu da dama.

Ko kuma

  1. Zai iya samar da ƙanan masana’antu da yawa
  2. Biya ɗalibai da yawa “Scholarship” da dubban ƴan arewa.

Za kai iya tunano wasu abubuwan ma da dama da zai taimaki Arewa in akai amfani da kuɗin da mu ke bawa ƴan kudu, a iya kuɗin “Mobile transfer” kaɗai. Ka lissafa ka gani.

Kuɗaɗen da ke barin Arewa ya koma kudu, na hadadar kuɗaɗe na bankuna, an ƙiyasta ya kai wajen tiriliyan 13, wanda ya ninnika kuɗin da Gwamnatin Tarayya ke bawa Arewa na kasafin kuɗaɗen ƙasa.

Wannan fa iya ɓangaren banki kenan fa kurum. Akwai i ɓangare da dama, kamar harkar layikan wayoyi, inshora, harkar karatu, kasuwanci dss.

Wannan ba abu ba ne da wani ko wasu ƙungiyoyi za su iya yaƙa ba ne. Magana ce ta manufar siyasar tattalin arziƙi da ya ke buƙatar siyasar tsare-tsare da aiki don shawo kan abun. Wannan na ɗaya daga cikin abin da ya sa arewa ke zama koma baya wajen tattalin arziƙi.
Talaucin Arewa na da alaƙa ta kai tsaye da rashin tasarrafi da kuɗaɗe da kuma ma’adananta.

Lallai ne ƴan Arewa su yi kira da a gyara tsarin kasuwanci, da yanayin gudunar da ayyuka a ƙasar nan. Ka bar farfagandar da ƴan kudu ke watsawa cewar wai ƴan arewa ci ma zaune ne. Miliyoyin ƴan Arewa na tashi daga bacci tun ƙarfe 4 na safe su fita nema har magariba don su samu ɗan wani don neman rufin asiri….

Kaɗan daga wani rubutu da na gani na yawo da turanci. Ni kuma Mukhtar Sipikin na fassara, fassara mai ƴanci.

Tags:
%d bloggers like this: