ABIN DA YA SA MASU GARKUWA DA MUTANE SUKA SAKO SARKIN KAJURU

  • Home
  • Labarai
  • ABIN DA YA SA MASU GARKUWA DA MUTANE SUKA SAKO SARKIN KAJURU

A ranar lahadi 11 ga Yuli ne jaridar Daily Trust ta sanar da sace Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu tare da iyalinsa guda goma sha uku a gidansa.

Amma kwana daya da kama sarkin, aka sako shi. Sai dai sun cigaba da tsare sauran iyalinsa da aka kama su tare.

Majiyarmu ta shaida mana cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi afuwar kama sarkin mai shekara 85 da suka yi a lokacin da suke mika shi ga mutanensa.

Kafin a sake shi ne, masu garkuwa da mutanen suka kira waya gab da magariba suka nemi a shirya karbar Sarkin. Wadanda suka je karbar sarkin sun isa inda aka gaya musu, a wani wuri da yake suka da garin Gengere, a inda suka ga uku daga cikin masu garkuwa da mutanen dauke da makamai cikin tufafin sojoji. A wannan lokacin ne suka nemi afuwar kama sarkin da suka yi.

 “Mun yi mamakin hakan. Sai kawai muka tsaya muna kallonsu a lokacin da suke neman afuwar, inda suka ce ba sa cikin natsuwa tun daga lokacin da suka kama shi. Sun ce mana mu tafi da shi, amma za a cigaba da tattaunawa a kan sauran mutane sha ukun kashegari (Talata).” A cewar majiyarmu wanda yake cikin wadanda suka je karbar Sarkin.

Daga samun labarin kubutar sarkin, mutanen gari sun fito kan titi suna nuna murnarsu na kubutar sarkin, inda aka ji wasu na fadin ‘maraba da adalin sarki.

Daga bincikenmu, ba a bada ko kwabo ba don sakin sarkin mai daraja ta biyu da ya hau mulki a shekara ta 1978.

Galadiman Majalisar Masarautar Kajuru wanda ke cikin ‘yan majalisa biyar na masarautar, Dahiru Abubakar ne ya tabbatarwa ‘yan jarida kubutar sarkin. Yanzu kuma sai jin yadda za a kare da sauran iyalin sarkin da aka cigaba da tsarewa.

Tags:
%d bloggers like this: