A RANAR ALHAMIS SHUGABA BUHARI ZAI KADDAMAR DA TITIN DOGO NA ZAMANI DA ZAI HADE KANO DA KADUNA

  • Home
  • Labarai
  • A RANAR ALHAMIS SHUGABA BUHARI ZAI KADDAMAR DA TITIN DOGO NA ZAMANI DA ZAI HADE KANO DA KADUNA

A ranar Alhamis ne ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da fara aikin titin dogo na zamani da ake kira ‘standard gauge’, wanda zai hada Kaduna da Kano.

Famanant sakatare na ma’aikatar sufuri ta kasa,Magdalene Ajani ne ya sanar da haka a ranar Talata a Abuja.

A sanarwar da ya fitar, za a yi bikin kaddamarwar ne a garin Zawaciki dake kananan hukumomin Kumbotso da Dawakin kudu da suke cikin jihar Kano.

Sanarwar ta kara da cewa wannan aiki zai bunkasa ayyukan shugaban kasa na hade kasar da layin dogo a kokarin habaka tattalin arzikin kasar.

An jima ana ta kiraye-kiraye a kan wannan aiki da wasu ke ganin tuntuni ya kamata a ce an fara shi.

Tags:
%d bloggers like this: