DEMOKARADIYYA ZA TA CIGABA DA ZAMA MARA MUHIMMANCI, MATUKAR BA ZA TA KAWO CIGABA KO ALHERI DA AKE FATA BA… FARFESA KAMILU SANI FAGE

  • Home
  • Labarai
  • DEMOKARADIYYA ZA TA CIGABA DA ZAMA MARA MUHIMMANCI, MATUKAR BA ZA TA KAWO CIGABA KO ALHERI DA AKE FATA BA… FARFESA KAMILU SANI FAGE

Farfesa Kamilu Sani Fage ya ce, wasu shugabanin na da kishin aiki amma ba su da kwarewa, wasu kuma na da kwarewar, amma ba su da kishin yin aikin. Farfesan kimiyar Siyasar ya yi wannan batu ne a yayin da yake gabatar da lakcha ta (Inaugural) ta Jami’ar Bayero, karo na 48 da aka gudanar a ranar Alhamis 8 ga Yuli, 2021, a babban dakin yaye dalibai na Jami’ar Bayero, Kano.

Farfesa Kamilu ya gabatar da rantsattsiyar takardar da ya bawa suna a turance da “From Dividends’ Optimism to Dashed Hopes: The Imperatives of Leadership Re-Engineering in Nigeria”. Ya gabatar da lacharsa ne tare da bada muhimmanci a kan demokaradiyya, shugabanci na gari da yadda za a sake fasalin shugabanci. Takardarsa ta yi waiwaye ne tun daga jamhuriyya ta daya a Najeriya har zuwa jamhuriyya ta hudu da ake ciki, wanda take cikin shekaru ashirin da biyu da kafuwa.

Malamin jami’ar ya kalli rashawa da cin hanci a matsayin wata babbar matsala da ta addabi kasar tun daga kafuwarta, walau a mulkin soja har zuwa na siyace. Malamin ya ce daga 1999 zuwa 2012, Najeriya ta yi asarar naira 1,354, 132, 400, 000.00, wato sama da naira triliyan 1.3 a rashawa da cin hanci a tsakanin tsofaffin gwamnoni da tsofaffin ministoci da tsofaffin ‘yan majalisa da tsofaffin ma’aikatan gwamnatin tarayya da na jihohi, sai kuma bangare harkar kudi da ‘yan kasuwa.

“Yan siyasa sun zargi sojoji da cin hanci da rashawa, amma rashawa da cin hancin da ake gani a zamanin demokaradiyya ya shafe abin da sojoji suka yi.” A cewar Farfesa Fage.

Ya kalli samar da shugabanci na gari a matsayin tsanin da zai iya fitar da kasar daga halin da take ciki, domin kundin tsarin kasar ya fayyace yadda za a tafiyar da komai da ya shafi shugabanci. Farfesa ya ce samun shugaban da zai aiwatar da tsare-tsare da kundin tsari ya fitar shi ne babban aiki.

Farfesa Kamilu Sani Fagge a tsaye yayin da Farfesa Ahmad M. Tsauni ke gabatar da shi

A bisa haka ne ya nemi da a sauya fasalin shugabancin kasar ta hanyar sauya tunanin shugabanni tare da horar da su a kan shugabanci na gari, yadda za su samu karkashin aiwatar da ayyukansu bisa gaskiya, amana da da’a.

A karshe ya ce demokaradiyya za ta cigaba da zama mara muhimmanci, matukar ba za ta kawo cigaba ko alheri da ake fata ba, na hidimtawa jama’a tare da sa shugabanni bautawa mabiyansu. Dole ne ‘yan Najeriya su dandani zakin da a duniya aka yayata demokaradiyya na da shi, sabanin haka zai sa ta fadi ba nauyi a kasar. A wata cewarsa, demokaradiyya ba za ta yi wata ma’ana ba har sai rayuwar talaka ta inganta, ta yadda wasu bukatunsa na dole a rayuwa ya same su.

Hakan kuma ba zai samu ba sai wakilan da jama’a suka zaba sun sadaukar da kansu don biyan bukatun wanda suke wakilta, ta hanyar rike gaskiya, dattako da yin komai a bude tare da soyayyar jama’a. Samun tabbatuwar wannan babban aiki, sai shugabannin sun kasance suna da ilimi da gogewar da za su alkinta dukiyar kasar don cigaba.

Zadeen Kano

Tags:
%d bloggers like this: