An Fitar da Sunayen Marubuta 11 Da A cikinsu Ɗaya Zai Lashe $100, 000 A Kan Gasar Adabi Ta NLNG

  • Home
  • Adabi
  • An Fitar da Sunayen Marubuta 11 Da A cikinsu Ɗaya Zai Lashe $100, 000 A Kan Gasar Adabi Ta NLNG

Kwamitin masu bada shawara na kamfanin ɗanyen gas na Najeriya, NLNG, wanda suke ɗaukar nauyin gasar rubutun adabi mafi daraja a Afirka, sun bayyana sunayen marubuta 11 da aka tantance kuma ake sa ran ɗayansu zai ci zunzurutun kuɗi har dalar Amurka, 100, 000 a matsayin awalajar gasar.


A sanarwar da Babban Manaja, mai kula da hulɗa da jama’a da ɗorewar cigaban kamfanin NLNG, Eyono Fatayi-Williams, ya sanar da sunayen mutanen 11 da aka tantance daga cikin mutane 202 da suka shiga gasar ta 2021.


Littattafan da aka tantance guda 11 sun ƙunshi: “Delusion of Patriots” na Obianuju V. Chukwuorji; da “Give Us Each Day” na Samuel Monye; da “Imminent River” na Anaele Ihuoma; da “In The Name of Our Father” na Olukorede S. Yishau sai “Mountain of Yesterday” na Tony Nwaka.


Sauran sun ƙunshi: “Neglected” na Lucy Chiamaka Okwuma; da “The Colours of Hatred” na Obinna Udenwa; da “The Girl with The Louding Voice” na Abi Dare; da “The Return of Half- Something” na Chukwudi Eze; da “The Son of The House” na Cheluchi Onyemelukwe-Onuobia; sai kuma “Your Church My Shrine” na Law Ikay Ezeh.


Ana sa ran za a fitar da sunayen mutane uku a watan Satumba, wanda daga bisani idan an samu zakara, kwamitin gudanarwa zai sanar da wanda ya lashe gasar a watan Octoba, 2021.


Wannan sakamako ya fito ne daga hannu shugaban alƙalan gasar na wannan shekara, Farfesa Toyin Jegede, wanda yake farfesa ne na adabin Turanci a Jami’ar Ibadan.
Sauran alƙalan sun haɗa da Farfesa Tanimu Abubakar, farfesan Turanci a Jami’ar Ahmadu Bello University, Zaria, da Dr. Solomon Azumurana, babban malami a sashen Turanci na Jami’ar Lagos.


Alƙalan sun aiyana sunayen da aka tantance a matsayin ingantattu da suka zo da sabon tunani wajen fuskantar abubuwa ta hanyar bada labari mai ƙayatarwa, tare da salo na musamman wajen gabatar darasi a rayuwar zahiri.
A cewarsu, “an samu cigaba na zahiri wajen kwarewar rubutu, wanda dole a yabawa NLNG da suka bada wannan dama ga marubuta don su yi bajakolin baiwarsu.”


Ita ma shugabar kwamitin gudanarwa ta gasar, Farfesa Akachi Adimora-Ezeigbo ta amince cewa sunayen mutane goma sha ɗayan kyakyawan zaɓi ne. Ta kuma yabawa alƙalan bisa aikin da suka gudanar na tantancewar.


An fara gudanar da gasar adabi ta NLNG a shekarar 2004, wanda ke karfafar marubuta a kowanne rukunin rubutu, inda ake jujjuya gasar duk shekara a tsakanin rubutun waƙe da zube da wasan kwaikwayo da kuma rubutun yara.


A lokaci guda kuma ana gudanar da gasar ne tare da kyautar awalaja ta NLNG a kan nazarin rubutuce-rubucen adabi, wanda kamfanin ke ɗaukar nauyi. Shi ma a 2020 an samu wanda suka shiga gasar guda huɗu. A wannan bangare na nazarin rubuce-rubucen adabi ana bada awalaja ta naira miliyan ɗaya.
Daga
Zadeen Kano

Tags:
%d bloggers like this: