Kungiyar Gwamnonin Jihohin Kudanci Najeriya Sun Gudanar Da Taro, Tare Da Daukar Mataki A Zartar Da Mulkin Karba-Karba A Najeriya

 • Home
 • Siyasa da Shugabanci
 • Kungiyar Gwamnonin Jihohin Kudanci Najeriya Sun Gudanar Da Taro, Tare Da Daukar Mataki A Zartar Da Mulkin Karba-Karba A Najeriya

Kungiyar gwamnonin jihohin kudancin Najeriya ta yanke shawara kan dole mulkin Najeriya ya zama na karba-karba daga Arewa zuwa kudu. Ta dau wannan mataki ne a taron da ta gudunar a ranar Litinin a birnin Ikko, a inda ta amince da wasu matakai daban-daban game da makomar kasar Najeriya.

Wannan sanarwa ta fito tab akin shugabansu Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo, inda suka jaddada goyon bayansu ga kasancewar Najeriya a matsayin kasa daya dunkulalliya.

Wani abin mamaki shi ne yadda suka kira taron nasu, dan lokaci kadan bayan gwamnatin Najeriya ta kamo Mr Nnamdi Kanu, mai rajin ballewa daga ƙasar Najeriya domin kafar ƙasar Biafra. Sannan da samame da jami’an tsaro masu farin kaya suka kai gidan Sunday Ogboho, shi ma mai rajin kafa kasar Yaraba ta Oduduwa.  

A takarda da gwamnonin suka fitar wanda Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ya sanya wa hannu ta fito da wasu matakai kan makomar Najeriya kamar haka:

 • Sun ce dole shugabancin Najeriya ya kasance na karba-karba daga yankin arewaci zuwa kudanci, kuma suna son shugaban kasa da za a zaɓa a 2023 ya fito daga yankin kudancin kasar saboda abin da gwamnonin suka kira tabbatar da adalci;
 • Gwamnonin kuma sun amince da wasu bukatu da suke son a aiwatar da suka shafi tsaro da yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima da kuma dokar man fetur;
 • Sun sake jaddada goyon baya ga hadin kan Najeriya;
 • Tabbatar da bukatar yan sandan jiha;
 • Dole ne duk wata hukumar tsaro ta nemi izininsu kafin kaddamar da samame a jihohinsu;
 • Kungiyar gwamnonin ta koka kan yadda a cewarta ake nuna son kai wajen tabbatar da adalci a Najeriya tana mai cewa ya kamata duk wanda za a kama a bi doron doka da ‘yancin dan kasa;
 • Sun tsayar da ranar 1 ga Satumban 2021 da dokar hana kiwo za ta fara aiki a dukkanin jihohin kudanci;
 • Ta yanke shawarar cewa dole a raba kudin da ake cirewa daga Asusun Tarayya na Gidauniyar ‘yan sanda ta kasa tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi;
 • Kungiyar gwamnonin ta yi fatali da matakin da majalisar dokokin kasar ta suka dauka na cire aika sakamakon zabe ta hanyar intanet daga dokokin zaben kasar;
 • Kungiyar kuma ta zabi Lagos a matsayin hedikwatar kungiyar gwamnonin kudancin Najeriya.
Tags:
%d bloggers like this: