Babban Hafsan Sojojin Najeriya Ya Yi Wa Jarumin Wasan Kwaikwayo, Samanja Kyautar Miliyan Biyu

  • Home
  • Labarai
  • Babban Hafsan Sojojin Najeriya Ya Yi Wa Jarumin Wasan Kwaikwayo, Samanja Kyautar Miliyan Biyu

A ranar Talata 6 ga watan Yuli, 2021 ne Babban Hafsan Sojojin Najeriya Manjo Janar Faruk Yahaya ya bada kyautar kudi, wuri na gugan wuri har naira miliyan biyu ga tsohon jarumin wasan kwaikwayo, Usman Baba Pategi da aka fi sani da ‘Samanja Mazan Fama.’

A yan kwanakin baya ne a kafofin sadarwar na zumunta aka samu wasu na yada jita-jita cewa jarumin ya riga mu gidan gaskiya, wanda hakan ya jan hankalin jama’a, har aka samu wasu ‘yan jarida da suka je gidansa dake Kaduna suka yi hira da shi, inda ya karyata zance da cewa idan da ya mutu yaushe za su zo su same shi har su yi hira da shi.

Babban Hafsan Sojojin Najeriya ya ce Samanja ya kasance mai kishin kasa, kuma mai wayar wa jama’a kai a fannin rayuwar soja da ta bariki. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa (COAS) ya bada wannan kyautar ne bayan ya ziyarci tsohon jarumin a gidansa dake Kaduna, inda shugaban ya samu wakilcin babban kwamandan GOC 1 Div ta rundunar soja a Kaduna.

Babban hafsan sojojin ya jinjinawa tsohon jarumin tare da yi masa fatan alheri da samun ingantacciyar lafiya, wanda ya ce an sanar da shi rashin lafiyarsa kuma ya ji ya zama dole ya bada tashi gudunmawa.

Ya kara da cewa jarumun ya taka rawa wajen daga darajar rundunar sojan a idon ‘yan Najeriya tare da nuna musu yadda rayuwa a bariki take, “Da wannan muhimmin rawa da ya taka, ya samarwa kansa wuri a masana’antar nishadi. Baya ga haka, ya kasance abun duba idan aka kira sunan rundunar sojin Najeriya,” Inji Babban Hafsan Sojan.

Shi ma Usaman Baba Pategi ya nuna farin cikinsa tare da mika godiyarsa da Babban Hafsan da ya tuna da shi. Ya yi kira ga sauran ‘yan Najeriya da su kasance masu kishin kasa tare da addu’ar zaman lafiya a Najeriya. Sannan jarumin ya yi kira ga matasa da su kasance masu ayyukan da zasu amfane su a rayuwa,

Tags:
%d bloggers like this: