Kungiyar Marubuta Ta Najeriya (ANA), Reshen Jihar Kano Ta Yi Bikin Rantsar Da Sababbin Shugabanninta

  • Home
  • Adabi
  • Kungiyar Marubuta Ta Najeriya (ANA), Reshen Jihar Kano Ta Yi Bikin Rantsar Da Sababbin Shugabanninta

A ranar Lahadi ne 4 ga watan Yuli, 2021 Kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA), reshen jihar Kano ta rantsar da sabbabbin shugabanninta da aka zaba a ranar 29 ga watan Mayu, 2021. An gabatar da bikin rantsuwar ne a dakin karatu na Murtala Muhammad dake Kano.


Farfesa Abdulkadir Dangambo, wanda yake uban kungiyar shi ya jagoranci taron tare da rantsar da sababbin shugabanin. Bayan rantsuwar, Dangambo ya shawarci sababbin shugabanin da su fitar da jadawalin ayyukan da za su gabatar a cikin tsawon shekara biyu da za su yi a wannan matsayi, don ya zama wani ma’auni da zai taimaka musu cimma burika da ayyuka da suka tsara.


Yayin jawabin maraba, tsohon shugaban ANA Kano, Mal. Zaharaddeen Ibrahim Kallah ya yabawa iyayen kungiyar da masu bada shawarwarin kungiyar tare wasu fitattun mambobi da suka bada gudunmawa sosai wajen tafiyar da kungiyar, tare da ganin an samu nasarori a tsawon lokacin da ya dauka yana shugabancin kungiyar. Kallah ya yi fatan cewa za su cigaba da bada irin wannan gudunmawa ga sababbin shugabanni.


Shi ma sabon shugaban ANA Kano, Tijjani Muhammad Musa, yayin da yake gabatar da sauran shugabanin kungiyar ga uban taron da sauran manyan baki, ya yi fatan cewa za su dora a kan ginin da aka yi wa kungiyar tare da shigo da sabon tunani wajen ciyar da kungiyar gaba. A cewarsa lokaci ya yi da ƙungiyar marubuta ba wai a Kano ba har kasa gaba daya za ta kai matakin kololuwar cigaba. Sannan ya ce, “gazawar marubuta ne idan har ba su ƙarfafi zukata da tunanin al’ummarsu ba,”


An yi bikin ranstuwar tare da gabatar da karatu na musamman, inda wasu fitattu kuma tsofaffin marubuta suka gabatar da karatu. Daga cikin wadanda suka yi karatu akwai, Mal. Nasiru G. Ahmad ‘Yan Awaki, da Hajiya Balaraba Ramat Yakubu da Mal. Ado Ahmad Gidan Dabino, MON da Mal. Ismail Bala da Mal. Habibu Hudu, sai Farfesa Faruk Sarkin Fada da Abba Danhausa.


A jawabin fatan alheri daga manyan baki, an ja hankalin sababbin shugabannin da su jajirce tare da dauriya wajen jagorancin kungiyar. Tsohon shugaban ANA Kano, Mal. Ismail Bala ya ce, a wajensa abu biyu suka fi wuya a duniya. ‘Horar da ‘yan wasan kwallon kafa a Birtaniya da shugabancin Kungiyar Marubuta ta ANA.’ Shi ma tsohon shugaban ANA Kano, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON ya nemi shugabannin da su fifita bukatun mambobinsu a kan nasu bukatun. Ya bada misali da a zamanin shugabacinsa aka sha gwagwarmaya da gwamnati har ya zamanto ana neman a tsare shi saboda kare hakkin marubuta.


Sauran wanda suka tofa albarkacin bakinsu tare da fatan alheri ga sababbin shugabanni sun hada da Farfesa Hamisu Darma da Hajiya Balaraba Ramat Yakubu da Farfesa Faruk Sarkin Fada da shugaban dakin Karatu na Kano, Dr. Ibrahim Bichi da Dr Bala Muhammad da Dr. Tijjani S. Almajir.


Tsohon Babban Daraktan Hukumar A Daidaita Sahu, Dr. Bala Muhammad ya shawarci kungiyar da ta fara gabatar da lacka a duk zango-zango na shekara, inda ya bada kan shi ga kungiyar don gabatar da lacka ta farko a kyauta.


Taron rantsar da shugabannin ya samu halartar marubuta da masana da dama da suka hada da Dr. Saka Aliyu da Dr. Jamilu Abdullahi da Hajiya Aisha Bilyaminu Usman da Kmared Rabiu Shamma da Kabiru Yusuf Anka da Abdulkarim Papalaji da Rabi’a Talle Maifata.


Daga shugabannin da aka rantsar akwai Maimuna Beli (Mataimakiyar shugaba) da Mazhun Idris (Magatakarda) da Danladi Z. Haruna (Ma’aji) da Yaseer Kallah (Mataimakin Magatakarda) da Abdullahi Kangala (Sakataren kudi) da Ibrahim M. Indabawa (Jami’in hulda da jama’a na Hausa) da Aliyu Abdullahi (Jami’in hulda da jama’a na Turanci) da Umma Sulaiman ‘Yan Awaki (Jami’ar walwala) da Hassan Ibrahim Gama (Mai bada shawara kan shari’ah) da Bilkisu Yusuf Ali (Mai binciken kudi I) da Sadiya Garba (Mai binciken kudi II). Akwai kuma shugabanni marasa gafaka da suka kunshi Dr. Murtala Uba da Abba Shehu Musa da Rufaida Umar sai Zaharaddeen Kallah.


Zadeen Kano

Tags:
%d bloggers like this: