Kano Pillars Ta Lallasa Lobi Star da 3-0

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da ake wa kirari da masu gida ta lallasa kungiyar Lobi Stars da ci 3 da nema, a wasan mako na 31 na gasar Firimiya ta Najeriya da ake bugawa. Masu gida sun samu wannan nasara ce a gidansu na wucin gadi dake jihar Kano, a filin wasa na Ahmadu Bello.

Kano Pillars ta ci kwallonta ta farko ta hannun Umar Hassan, tun kafin a tafi hutu rabin lokaci, sannan David Ebuka ya kara kwallo ta biyu. Kwaftin din kungiyar Rabi’u Ali ne ya jefa mata kwallo ta uku.

Yanzu dai Kano Pillars tana da maki 55, inda take a matsayi na biyu a kan teburi, a inda kungiyar Akwa ke kan tebirin da maki 57.

%d bloggers like this: