Shugaban Kamfanin BUA Ya Bada Kyautar Hannun Jari Ga Ma’aikatansa Na Sama Naira Biliyan Biyu

  • Home
  • Kasuwanci
  • Shugaban Kamfanin BUA Ya Bada Kyautar Hannun Jari Ga Ma’aikatansa Na Sama Naira Biliyan Biyu

Shugaban kamfanin BUA abdulsamad Isyaka Rabiu, wanda yake da mafi girman hannun jari a kamfanin siminti na BUA Cement Plc ya sanar da yi wa ma’aikatansa tagomashin kyautar hannun jarin kamfanin ga wasu ma’aikatansa.

Ya bada wannan hannun jarin ne da kuɗinsa ya kai naira biliyan biyu, saboda irin gudunmawar da ma’aikatan suka bayar wajen ganin kamafanin ya cigaba da samun riba, duk da annobar da aka shiga tare da hasashen shekarar za ta zo da ƙalubale.

“Abin kulawa ne, duk da annobar da aka shiga, kamafin simintin na BUA ya kasance ɗaya daga cikin kamfanoni da suka fi cin riba a Najeriya, inda ya gabatar da riba ta naira biliyan 72.3, bayan cire haraji, inda aka samu ƙarin kaso 19.4% da ya nuna ƙaruwa, idan an yi la’akari da shekarar baya ta 2019.” Kamfanin ya sanar da haka a bayanan da AMON NASARA ta samu.

A sanarwar da ofishin shugaban kamfanin ya bayar, Abdulsamad Rabiu ya ce yana da matuƙar mihimmanci a yaba da irin gudunmawar wasu fitattun ma’aikata, wanda suka dinga aiki ba dare ba rana, duk da annobar da aka sha fama a 2020,.don ganin kamfanin ya ƙara ƙarfi duk da tagomashi da kyakkyawan harsashin cigaba da yake da shi.

“A ƙoƙarinmu na shiga wata shekarar mai cike da riba, bada wannan hannun jari ga ma’aikatanmu shi ne kaɗai abin da ya dace mu yi. Yin haka zai sa zakwaƙuran ma’aikatanmu amfana da nasara da cigaban da za a samu, wanda za su cigaba da taimakawa wajen samuwar hakan.” inji Alh. Rabiu.

Tags:
%d bloggers like this: