Ilimi Kyauta Kuma Dolen Da Gwamnatin Kano Ta Aiwatar, Yaudara Ce Kawai- Shugaban Kungiyar Makarantun Sa Kai Ta Jihar Kano

  • Home
  • Labarai
  • Ilimi Kyauta Kuma Dolen Da Gwamnatin Kano Ta Aiwatar, Yaudara Ce Kawai- Shugaban Kungiyar Makarantun Sa Kai Ta Jihar Kano

An zargi gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da laifin ruguza ilimi a jihar Kano. Wannan batu ya fito ne ta bakin shugaban Kungiyar Makarantun Sa Kai Ta Jihar Kano, Awwalu Hussaini Ayagi, wanda ya fadi haka a tashar gidan Radiyo Freedom a yau Litinin.

Shugaban ya ce ilimi kyauta da Gwamnan Kano ya kawo ba wani abu ba ne illa wata hanya da za ta rusa ilimin jihar, wanda ya kalli shirin a matsayin yaudara da rashin gaskiya.

“Ai dama wannan shirin ba da limi kyauta kuma dolen da gwamnatin Kano ta aiwatar, yaudara ce kawai gwamnatin ta yi wa jama’a, don su rinka ganin kamar taimakonsu aka yi, kuma gaskiya ba wani taimako da gwamnati ta yi sai ma rugurguza harkar ilimi.” In ji Shugaban.

A bisa wannan dalili ne Mal. Awwal yake ba wa iyaye shawara kan kar su sakankance su ki shiga lamarin karatun ‘ya’yansu don ganin an ce ilimi kyauta ne.

“Shi ya sa yanzu muke son jan hankalin jama’a kar su saki jiki cewa, yanzu gwamnati ta bai wa ‘ya’yansu ilimi kyauta su ki taimakawa ‘ya’yansu, wannan shi ne illar ilimi kyauta, shi ne ya sa yara suke faduwa a jarrabawa.”

Shugaban ya kara zargin faduwa mai yawa da aka samu a jarrabawar tantancewar rubuta jarrabawar karshe da aka samu a jihar Kano da laifin wannan tsarin na jihar Kano.

“Yanzu dubi kamar wannan jarabawa ta qualifying din nan da dalibai suka fadi a kwanan nan, duk matsalar ilimi kyauta ta janyo.”

Tags:
%d bloggers like this: