An Shirya Yi Wata Daɗaɗdarar Gawar Misra Gwajin Zamani Mai Gani Har Hanji

  • Home
  • Labarai
  • An Shirya Yi Wata Daɗaɗdarar Gawar Misra Gwajin Zamani Mai Gani Har Hanji

An fara gwaje-gwajen gani har hanji a kan wata daɗaɗdar gawar Misra (mummy) a wani asibiti dake birnin Milan dake Italiya, a ranar Litinin 21 Ga Yuni, 2021 don yin bincike tare da gano tarihinta.

Wannan na cikin ƙoƙarin binciken da ake don gano yadda kamanin gawar yake da yadda ta yi rayuwa har zuwa mutuwarta, ta hanyar amfani da na’urar zamani mai gani har hanji da a Turance ake kira (CT Scan).

Ita wannan gawa ana tunanin tana daga cikin shugabannin addini dake hidimtawa ubangijin Misirawan dauri, wanda ake wa laƙabi da Ankhekhonsu. Tuni dai an fara gwajin a asibitin Piliclinico, bayan an ɗauko gawar daga gidan tarihi na Bergamo.

“Wani tsari ne na bincike da tantancewa. Za mu iya bincikawa har cikin gawar don nazartar yadda take, za mu iya ƙirƙirar mata rayuwa da mutuwa, tare da gano ainahin jinsinta ta hanyar nazartar ƙashin kwankwasonta tare da auna tsayinta don mu fahimci ainahin tsayinta.” A cewar Sabina Malgora, Daraktan wannan binciken gawar ta mummy.

Ma’aikatan lafiya na asibitin suma sun gudanar da wani bincike ta hanyar amfani da sinadirai a kan gawar don gano abubuwan da aka yi amfani da su wajen daskarar da jikinta.

“Gawarwakin mummies wani abin tarihi ne don nazarin kai tsaye a kan halittu. Kamar wani kwafso ne na lokaci da za mu iya fahimta,” A cewar Malgora.

Misirawan dauri na kiran Ankhekhonsu da ma’ana ‘ubangiji Khonsu na raye’, an san hakan domin an rubuta hakan a jikin akwakun gawar sau biyar. Malgora ya ce akakwun ya wanzu a daula 22 da suka gabata tsakanin shekaru 900 da 800 kafin haihuwar Annabi Isa.

Ana zaton gawar na cikin manya masu hidimtawa ubagijinsu, amma Malgora ya ce wannan bincike mai gani har hanji zai tabbatar da haka ko akasin hakan.

A watan Afirilu an gudanar da wani bincike makamancin wannan da naura mai gani har hanji a kan wata gawar da ake tsammani namiji ne, daga cikin manyan masu hidintawa ubangijinsu. Amma sai masanin kimiyyar ƙasar Polish a Warsaw ya gano ashe gawar mace ce mai ɗauke da tsohon ciki dake da shekaru ƙasa da talatin.

%d bloggers like this: