YA KAMATA KAMFANIN TUWITA YA MUTUNTA KANSA

  • Home
  • Tsokaci
  • YA KAMATA KAMFANIN TUWITA YA MUTUNTA KANSA

Na yi tunanin za a zo ga wannan mataki na dakatar da kamfanin Tuwita daga yin aiki a Najeriya. Duk da cewa jama’a na da ‘yancin fadar albarkacin bakinsu, amma komai akwai dokoki da tsari a cikin wannan tafiya.

Kamfanin Tuwita a Najeriya yana da ɗinbin masu amfani da shi, wanda hakan na nufin yana samun ribar mai tsoka, fiye da duk wata ƙasa a Afirka.

Idan har suna amfana da Najeriya, kamata ya yi su mutunta yarjejeniyar kasuwanci, wanda a ko’ina a duniya suke rattabawa don amincewa da dokokin ƙasa da kasuwanci.

Wannan magana ta wuce goge rubutun shugaba Buhari. Duk wanda yake bibiyar shafikan ‘yan ƙungiyar IPOB, yana ganin rubuce-rubuce na tunzura da batanci ga mutanen Arewa, wanda suke ganin kamar mukullin darewar Najeriya yana hannunsu.

Duk irin waɗannan rubuce-rubuce, ba wani mataki da aka ɗauka. Daga lokacin da aka bada sanarwar goge rubutun shugaba Buhari, na yi ƙoƙarin shiga shafin Nmandi Kanu, wanda har a lokacin na ga rubuce-rubuce da suka saɓa dokoki da su Tuwita ke iƙirari. A lokacin na fitar da guda biyar tare da jan hankalin kamfanin, duk da cewa sun amsa min za su duba, amma babu wani abu da ya biyo baya.

Daga abubuwan da suke faruwa a yanzu a kudu maso gabas zai tabbatar maka IPOB sun samu abin da suke so na goyon bayan Tuwita da shi mamallakin Jack.

A ‘yan kwanakin nan mutanen Arewa sun tafka asara a kudu maso gabas, saboda ƙona motocin kaya tare da daka wasoso. Wani abin takaici wanda da na gani, idan har a wannan lokaci ya faru zan iya cewa muna cikin barazana sosai. Motar tirela na gani ta ɗebo shanu zuwa can kudu, wanda aka kunna mata wuta tare da shanun. Motar da shanun na cin wuta, har za ka wasu na ƙoƙarin fita yayin da suke ci da wuta. Inna lillahi wa’ina ilaihir rajiun. Wanda zai yi wa dabbobi haka, babu abin da ba zai iya ba. Wannan al’amari idan a Arewa aka yi sai duniya ya ɗau ɗimi, ana maganar ‘yan Arewa jahilai ne.

Mun ga irin rawar da Tuwita ya taka a zanga-zangar EndSars, wanda duk dokoki na kamfanin na rashin yadda a nunawa hotuna jini da kashe-kashe, Tuwita ya yarda an dinga yaɗa irin wanɗannan hotuna na bogi,wanda wasunsu ba a ma ƙasar suka faru ba, wasu kuma ɗalibai ne ke gabatar da wasan kwaikwayo.

Wannan dakatarwar ba wani abin tada jijiyar wuya ba ne, idan har tuwita zai yi gyara na yadda yake gudanar da ayyukansa a Najeriya. Dole su kalli abin da suke yi na ba daidai ba, da Bature ya kira ‘double standard).

Bana jin wannan dakatarwar za ta jima, domin su ma ba za su so rasa gwaggwaɓar ribar da suke kwasa a Najeriya ba.

Daga

Zaharaddeen I. Kallah

%d bloggers like this: