Jirgin Ethiopian Zai Dawo Aiki A Kano Da Enugu

  • Home
  • Labarai
  • Jirgin Ethiopian Zai Dawo Aiki A Kano Da Enugu

Kamfanin jirgin saman Ethiopian Airlines ya sanar cewa zai dawo aiki a filin jirgin sama kasa da kasa na Kano da Enugu, da zarar an kaddamar da sababbin sashen da aka gina don zirga-zirgar jiragen kasashen waje.

A satin da ya gabata ne wani jirgi na musamman na kamfanin Ethiopia ya sauka a filin jirgi na Malam Aminu Kano International Airport (MAKIA), wanda hakan na cikin shirye-shiryen bude gurin.

Tun da aka rufe filin jirgin na Aminu Kano, gwamnatin tarayya ke shan matsin lamba kan a gaggauta bude filin jirgin.

Kafin kullen annobar Korona, jirgin Ethiopian yana aiki a jihohi hudu a Najeriya da suka hada da Lagos da Abuja da Kano sai Enugu.

Babban Manajan jiragen Ethiopian a Najeriya, Shimeles Arage, a sanarwar da ya fitarwa ‘yan jarida, ya ce kamfanin zai samar da jirgin da zai dinga jigila a Kano da Enugu.

“Ethiopian ya fara aiki a Najeriya tun 1960, wanda da dadi ba dadi yana tare da Najeriya na tsawon wannan lokaci.” Inji Arage.

%d bloggers like this: