Sojojin Najeriya Sun Murtsuke Mayaƙan Dake Ikrarin Alaƙa Da Ƙungiyar IS

  • Home
  • Labarai
  • Sojojin Najeriya Sun Murtsuke Mayaƙan Dake Ikrarin Alaƙa Da Ƙungiyar IS

Sojojin Najeriya sun bayyana nasara da suka samu a kan mayaƙan dake ikrari jihadi da alaƙa da ƙungiyar IS, a inda suka karkashe mayaƙan da lalata motocinsu guda bakwai a Marte ɗauke da makamai a jihar Borno.


A lokaci guda rundunar sojojin ta musanta rahotannin dake yawo cewa mayaƙan sun fatattaki sojojin Najeriya a sansaninsu dake kusa da Marte.

Maii magana da yawun rundunar sojan Birgediya Janar Bernard Onyeuko ya ce sojojin sun janye ne daga sansanin dake kusa da Marte, don yin kwanton ɓauna ga mayaƙan. Hakan kuwa ya sa sun faɗa wannan tarko, inda suka ƙaddamar masu da hari, tare da lalata ayarin motocinsu dake dauƙe da muggan makamai.

Wannan ƙungiyar ta ISWAP ta addabi jami’an tsaro da farar hula a gabashin Najeriya. Haƙiƙa wannan nasara za ta ƙarawa sojojin Najeriya azama na gamawa da waɗannan ɓata gari.

Tags:
%d bloggers like this: