Ƙungiyar Waiwaye Adon Tafiya Ta Karrama Wasu Mutane A Taron Bikin Cikarta Shekaru Shida

  • Home
  • Labarai
  • Ƙungiyar Waiwaye Adon Tafiya Ta Karrama Wasu Mutane A Taron Bikin Cikarta Shekaru Shida

A ranar Litinin 11/1/2021 ne ƙungiyar raya harshe da al’adun Hausawa mai suna Waiwaye Adon Tafiya dake birnin Kano ta gabatar da bikin cikarta shekaru shida da kafuwa, wanda aka gudanar a gidan tarihi na Makama. Ƙungiyar Waiwaye Adon Tafiya na bisa jagorancin Alhaji Ibrahim Muhammad Mandawari, wanda ke amfani da kwarewarsa da gogewa a rayuwa wajen ba ta shugabanci na gari tare da shigo da abubuwa da za su bunƙasa al’adu, adabi da harshen Hausa..

An gudanar da taron bikin ne bisa jagorancin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau na Jam’ar Bayero, Kano. Shugaban taron ya yabawa ƙungiyar a biisa ƙoƙarinta na bibiyar al’amuran da suka shafi al’adun Hausawa, wanda suka shahara a duniya. Sai dai Farfesa Gusau ya koka yadda wasu baƙin al’adu ke yin kutse a cikin Hausawa, wanda ke sauya musu tsarin rayuwa da aka sansu da shi shekaru aru-aru.

Ita ma Dr Asiya Malam Nafiu ta kwalejin tarayya ta Kano (FCE), wacce ta kasance mai jawabi a gurin ta yi jawabi ne a kan taken taron na bana da aka kira ‘A san mutum a kan cinikinsa.’

Dr Asiya ta yi bayani yadda harshen Hausa ya samu tagomashi a ɓangaren sana’oi. To amma riƙon sakainar kashin da Malam Bahaushe ya yi wa sana’oinsa, ya sa bai inganta su ba, yadda za su tafi da zamani. Malama ta kawo matsalar satar fasaha a matsayin babbar matsala da sana’oin Hausawa ke fuskanta.

Ta buƙaci shigowar hukuma a matsayin babbar hanya da za a iya magance wannan matsala. A cewarta hakan zai kara bunƙasa harshen fiye da yadda ake tunani

Masu ta’aliƙi a gun taron Farfesa Yakubu Magaji Azare da Dr Umma Aminu Inuwa sun yi jawabinsu ne a kan yadda ya kamata Hausawa su yi riƙo da sana’oinsu tare da martabasu. Hakan ba zai samu ba sai da ilimi, wanda shi zai buɗe musu ƙofa. A cewar Farfesa Azare, ilimi shi ne babban mabuɗi da zai kawo wa sana’oin Hausawa ci gaba har a yi gogayya da su a duniya.

Shi ma uban taro, mai girma Dan Majen Kano, Hakimin Gwale Alh. Yahaya Inuwa Bayero ya yi tsokaci ne kan yadda za a tafi da zamani, tare da shigowar mutane masu zaman kansu wajen abubuwa da suka shafi raya al’adu. “Gwamnati kaɗai ba za ta wadatar da buƙatar da ake da ita ba a abin da ya shafi raya al’adu.” A cewarsa Hakimin Gwalen.

Dan Majen Kano ya bada misalai na yadda ake samun musayar fasaha da ilimi a ƙasar Hausa. Ya bada misali da zamanin Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi da aka tura wasu mutane gabashin duniya don su koya wasu sana’oi da yanzu ake alfahari da su a ƙasar Kano.

Kwamishinan raya al’adu da yawon buɗe ido na jihar Kano, wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar ya yabawa ƙungiyar a kan ƙoƙarinta na wannan aiki wanda ke da alaƙa sosai da ma’aikatarsu. Ya ce ƙofarsu a buɗe take ga kowa, kuma kwanannan za su gaiyaci ƙungiyoyi da masana domin yin wani zama da zai bada dama a yi wani a abu da zai bunƙasa al’adu da sana’oi.

Sannan ya ƙara da cewa, “Ina tabbatarwa masana da suka yi jawabi tare da bada shawara ga gwamnati cewa za mu tabbatar an aiwatar da aƙalla ɗaya ko biyu na shawarwari da suka bayar.”

Tun farko, yayin jawabin maraba, shugaban ƙungiyar Waiwaye Adon Tafiya, Alhaji Ibrahim Mandawari ya yi maraba ga mahalarta taro, tare da bayyana irin ayyukan da ƙungiyar take aiwatarwa.

Shugaban ya ce ban da tarurrukan da suke gabatarwa na musayar ilimi da raya harshen Hausa da al’adu, ƙungiyar Waiyaye Adon Tafiya na yin abubuwa da suka jiɓanci gina rayuwar al’umma tare da ziyartar asibitoci don tallafawa marasa lafiya da yin taron addu’oi ga ƙasa da sauransu.

A ƙarshe ƙungiyar Waiwaye Adon Tafiya ta karrama wasu mutane da takardar shaidar girmawa, saboda irin gudunmawar da suke bayarwa a kan harshe da al’adu da ciyar da al’umma gaba. Daga cikin waɗanda aka karrama akwai shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA), reshen jihar Kano; Zaharaddeen Ibrahim Kallah da tashar Arewa Radiyo da Mal. Muhammadu Hussaini Gala Sumaila da Muhammad Umar Kaigama da sauransu.

Tags:
%d bloggers like this: