Idan ɗan fim ya saki matansa a shirin fim, saki ya tabbata a matansa na zahiri

  • Home
  • Tsokaci
  • Idan ɗan fim ya saki matansa a shirin fim, saki ya tabbata a matansa na zahiri

Wata fatwa da Dr Bashir Aliyu Umar, babban limamin masallacin Alfurqan ya bayar na cigaba da yamutsa hazo a duniya, musamman a kafofin sada zamunta.

Dr Bashir a cikin karatunsa ya tabbatar da cewa idan miji a cikin shirin Fim ya saki matansa, to wannan saki ya tabbata a kan matasa na gida idan yana da su.

Wannan fatawa ta kasance mahawara mafi zafi da ake tattaunawa tun daga fitarta. Da yawa daga cikin waɗanda ke harkar fim sun ƙalubalanci wannan fatawa.

Amma wasu na ganin wataƙila akwai abin da malam ɗin yake son cewa, wanda dole a ji ba’asi daga gurinsa.

Idan an tafi akan wannan fatawar, da yawa daga cikin ‘yan fim sun saki matansu ya fi sau shurin masaƙi.

Tags:
%d bloggers like this: