Kamfanin Twitter ya rufe kafar shugaban ƙasa Donald Trump na dindindin

  • Home
  • Kasashen Waje
  • Kamfanin Twitter ya rufe kafar shugaban ƙasa Donald Trump na dindindin

Twitter ta dakatar da kafar sadarwar shugaban ƙasar Amurka Donald Trump a ranar juma’a, saboda tada zaune tsaye.
Wannan dakatarwar ta kasance ta dindindin, domin ko a ranar 6 ga Janairu, 2021 an dakatar da shi na wucin gadi har awa 12. Amma hakan ba ta sa ya saduda ba.

Trump ya yi amfani da kafar twitter wajen cin zarafin mataimakin shugaban ƙasa Mike Pence a lokacin da magoya bayansa suka tada zaune tsaye a Capitol.

Kamfanin Twitter ya tabbatar da dakatar kafar @realDonaldTrump gaba ɗaya, saboda kare rashin jin daɗi da rashin yin hakan zai cigaba da kawo wa.

Tags:
%d bloggers like this: