A Cigaba Da Tsare Omoyele Sowore – Inji Kotu

  • Home
  • Labarai
  • A Cigaba Da Tsare Omoyele Sowore – Inji Kotu

Wata kotun majistire a Abuja ta bada izinin a cigaba da tsarr bayar da umarnin a ci gaba da tsare Omoyele Sowore, ɗan gwagwarmayar kuma mawallafin jaridar Sahara Repoters, a Gidan Gyara Hali na Kuje dake birnin tarayya Abuja.

‘Yan sanda ne suka gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin yin taro ba tare da izini ba da kuma uzura wa mutane. An tsare shi ne tare da wasu mutane guda huɗu.

Amma dukkaninsu sun musanta zargin da ake yi musu, kuma za a ci gaba da tsare su har zuwa gobe Talata domin sauraron ƙudirin neman beli.

Idan ba a manta ba Sowore ya jagoranci wata zanga-zanaga a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata.

Tags:
%d bloggers like this: