Mun Yi Ruwan Wuta A Dajin Sambisa Tare Hallaka ‘Yan Ta’adda- Shalkwatar Tsaron Najeriya

  • Home
  • Labarai
  • Mun Yi Ruwan Wuta A Dajin Sambisa Tare Hallaka ‘Yan Ta’adda- Shalkwatar Tsaron Najeriya

Rundunar sojan Najeriya ta sanar da mutuwar wasu ‘yan ta’adda a dajin Sambisa na jihar Borno, bayan da jiragen yakinta suka yi ruwan wuta ga ‘yan ta’addan.

Shalkwatar tsaro ta sojojin Najeriya ta ce sun gabatar da aikin ne karkashin rundunar Operation Lafiya Dole, wanda ya samu nasara yin barna sosai ga gungun ‘yan ta’addan.  

Mai magana da yawun shalkwatar tsaron, Manjo Janar Enenche, wanda ya fitar da wata sanarwa a ranar Talata ya ce jiragen yaki na rundunar sojan saman ta yi ruwan wuta a cikin zuciyar dajin Sambisa a ranar Litinin.

Sanarwar ta bayyana yadda jiragen suka lalata wasu sansani da yake maboya ga ‘yan ta’addar tare da kashe da yawansu.

“Jirgin rundunar sojan saman ya mamayi sansanin cikin nasara, wanda hakan ya yi sanadiyar rugurguza gine-gine da kayan yaki, tare da wani guri da ake zargin sashe ne na manyan bindigu dake kakkabo jirage, musaman yadda ‘yan ta’addan suka yi kokarin harbo jirgin sama rundunar sojan saman Najeriya. Da yawa daga cikin ‘yan ta’addan an gama da su.” Sanarwar ta ce.

Tags:
%d bloggers like this: