‘Yan Jarida na Allah wadai da hukunci da aka yi Zhang Zhan a kan rahoton corona virus

  • Home
  • Kasashen Waje
  • ‘Yan Jarida na Allah wadai da hukunci da aka yi Zhang Zhan a kan rahoton corona virus

‘Yan jarida a fadin duniya na Allah wadai da hukuncin da aka yankewa wata ‘yar jarida Zhang Zhan, ‘yar shekara 37 a kasar China saboda bada rahoto a kan cutar korona da ta balle a kasar. Kotu ta yanke mata shekaru 4 a gidan kaso bisa zargin cewa ta ba da rahoto da ba haka yake ba.

Zhang a watan Fabrairu ne ta tashi daga garinta a Shanghai har birnin Wuhan, inda ta samu bayanai a kan cutar korona tare da daukar hotuna da hoto mai motsi na halin da ake ciki a kan cutar. Amma hakan ya fusata gwamnatin kasar, wanda abubuwan da suka fada ya yi karo da nata labarin.

Yanzu dai ana kalubalantar kasar China bisa wannan hukunci da yake take hakkin dan adam.

Tags:
%d bloggers like this: