Fitatcen Ɗan Jarida, Mawallafin Jaridun Leadership Sam Nda-Isaiah Ya Mutu.

  • Home
  • Labarai
  • Fitatcen Ɗan Jarida, Mawallafin Jaridun Leadership Sam Nda-Isaiah Ya Mutu.

An tashi da alhinin rashin Sam Nda-Isaiah, wanda yake mawallafin gungun kamfanin jaridu na Leadership. iyalansa ne suka sanar da mutuwarsa da misalin karfe 11 na daren jiya Juma’a, bayan wata gajeruwar rashin lafiya.

Mista Sam wanda yake haifaffen jihar Niger, kuma yake riƙe da sarutar Kakakin Nufe ya mutu yana da shekara 58.

A taɓa yin takarar shugabancin ƙasa a shekara 2015, yayin da jam’iyar APC ke ƙoƙarin fidda ɗan takararta.

‘Yan jaridar ƙasar nan sun shiga jimami na rashinsa. Tuni fadar shugaban ƙasa ta saki saƙon ta’aziyya na wannan rashi da aka yi.

Tags:
%d bloggers like this: