Jami’ar East Carolina Ta Ba wa Ganduje Hakuri

  • Home
  • Labarai
  • Jami’ar East Carolina Ta Ba wa Ganduje Hakuri

A satin da ya gabata ne aka shiga wani rudani da ka-ce-na-ce a kafofin sadarwa sakamakon wata takarda da ta fita na cewa Jamiar East Carolina ba ta ba wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje damar koyarwa a matsayin Farfesa mai kai ziyarar koyarwa jami’ar. Wannan ne ya sa Gwamma Ganduje ya nemi Jami’ar ta bashi hakuri, saboda rashin jin dadi da tozarci da hakan ya janyo masa.

Shugaban jami’ar Grant Hayes ya aiko da wata wasika ga Dr. Ganduje da aka sa wa hannu a ranar 8 ga watan Disamba, 2020 inda ya ce gwamnan ya cancanci a bashi matsayin duba ga matsayin karatunsa.

Shugaban ya ce ba da niyyar cin mutuncin Ganduje ya mayar da martani kan labarin nadashi Farfesa ba. Ya ce sun samu sakon da gwamnan ya tura ranar 7 ga Disamba, 2020, da irin kwarewar da yake da ita. Grant yace. “Na yi takaicin duk wani irin cin mutuncin da haka ya janyo maka.”

Mun yarda ka yi karatu sosai, amma kayi hakuri: Jami'ar East Carolina ta baiwa Ganduje hakuri

Tags:
%d bloggers like this: