An dakatar da kamfanonin waya daga sayar da sababbin layuka a Najeriya

  • Home
  • Labarai
  • An dakatar da kamfanonin waya daga sayar da sababbin layuka a Najeriya

Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya, Nigerian Communications Commission (NCC), ta sanar da dakatar da sayar da sababbin layukan waya a fadin kasar. Ta bada wannan umarnin ne ga kamfanonin sadarwa dake da lasisi a kasar a wata wasika da ta fita ranar Litinin

Kafar sadarwa ta BBC Hausa ta ruwaito wannan dakatarwa na da nasaba da aikin duna rumbun bayanan rajistar masu layuka da ake, kuma wannan umarni zai cigaba har sai aikin ya kammala.

“Bisa umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar na tabbatar da an bi tsarin yi wa layuka rajista, hukumar ta duƙufa kan tantance rajistar masu layuka domin ta tabbatar da an bi umarnin sannan ta daidaita ayyuka,” a cewar daraktan ayyukan NCC, A.I. Sholanke, wanda ya sanya hannu a wannan wasika.

“Saboda haka, an umarce ku da ku dakatar da sayarwa da kuma ƙaddamar da sabbin layukan kamfaninku har zuwa sanda za a kammala binciken.

“Sai dai kuma idan ya zama dole, za a iya bayar da umarni na musamman idan an samu amincewar gwamnatin tarayya ta hannun hukumar NCC.”

A gefe daya hukumar ta gargaɗi kamfanonin a kan idan suka saba wannan umarni, za a iya ƙwace lasisin gudanar da ayyukansu.

An dauki wannan mataki ne saboda masu amfani da layukan marasa rajista da cikakken bayanai wajen aikata muggan laifuka.

Tags:
%d bloggers like this: