Wa ake sa ran za ta zama gwarzuwar gasar gajerun labaran hikayata, na BBC Hausa?

  • Home
  • Gajerun Labaru
  • Wa ake sa ran za ta zama gwarzuwar gasar gajerun labaran hikayata, na BBC Hausa?

A yau Juma’a ne ake sa ran za a sanar da wacce za ta dauki kambun gwarzuwar gasar gajerun labarai ta mata zalla, wato Hikayata ta 2020, a bikin da za a gudanar a Abuja, Najeriya.

Kafar BBC Hausa ta sanar cewa za a fitar da gwarazan da aka tantance daga labarai sama da 400, a matakai daban-daban don fitar da guda uku da alkalan gasar suka ce sun yi zarra.

A wajen wannan babban biki ne za a ambaci labarin da ya yin na daya zuwa uku, inda duk duk za a karrama wadannan marubuta guda uku.

Wannan marubuta guda uku sune, Rufaida Umar Ibrahim da Surayya Zakari Yahaya sai Maryam Umar. Ga kadan daga cikin abin da labaran nasu suka kunsa.

Labarin ‘Farar Kafa’ na Rufaida Umar Ibrahim

Wannan labari ne kan wata wadda yarda da camfi ya jefa ta a cikin mawuyacin hali.

Bayan aurenta mijinta ya yi ta gamuwa da jarrabawa iri-iri kuma ya camfa cewa tana da farar ƙafa shi ya sa waɗannan iftila’i ke hawa kansa.

Rahama ta sha tsangwama dalilin haka kuma aka yi mata laƙabi da mai farar ƙafa.

Labarin ‘Rai da Cuta’ na Maryam Umar

Labarin Rai da Cuta ya duba yadda mutane ba su yarda da cutar korona ba, cutar da ta zama annoba a duniya.

Tauraruwar labarin mace ce mai juna biyu da mijinta ya kamu da cutar korona amma ya ƙi kai ta asibiti har ita ma ta kwashi cutar.

Mijin nata ya kulle ta a ɗaki har ta kusa rasa ranta sannan jaririn da ke cikinta ya mutu.

Labarin ‘Numfashin Siyasa’ na Surayya Zakari Yahaya

Numfashin Siyasa labari ne kan wata matashiya da ta yi ƙoƙarin ceto al’umar ƙauyensu ta hanyar shiga siyasa. Sai dai al’umarta ba ta shirya morar shugabanci daga hannun mace ba don haka sai ta juya mata baya.

A gwagwarmaryar siyasar ta, tauraruwar labarin ta rasa iyayenta sannan ta fuskanci tsangwama da wulaƙanci daga mutanen ƙauyenta.

Alkalan Gasar

Alkalan da suka yi aikin fitar da gwarzayen a wannan shekara sune Hajiya Bilkisu Salisu Ahmed Funtua; gwana a rubutun Hausa da Dokta Hauwa Bugaje, malama a tsangaya harsunan Afrika a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, sai kuma marubuci kuma dan jarida mai zaman kansa Sada Malumfashi.

Duk wacce ta yi nasara ita ce za ta zama ta gwarzuwa ta biyar a jerin gwarazan gasar, tun daga shekarar 2016, kuma za ta karbi kyautar kuɗi dala 2,000 da lambar yabo.

Wadda ta zo ta biyu kuma za ta karɓi kyautar kuɗi dala 1,000 da lambar yabo, sannan wadda ta yi ta uku za a ba ta kuɗi dala 500 da lambar yabo.

Tags:
%d bloggers like this: