Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar Da Hukunci Kisa Kan Maryam Sanda

  • Home
  • Labarai
  • Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar Da Hukunci Kisa Kan Maryam Sanda

A yanzu haka Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Najeriya ta kori ƙarar da Maryam Sanda ta shigar gabanta tana neman a hana aiwatar da hukuncin kisan da wata Babbar Kotu ta yanke mata.

Wannan Kotun ita ma ta jaddada hukuncin da Babbar Kotun ta Abuja ta zartar na yanke wa Maryam hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Hakan na nufin kotu ta yarda cewa wacce aka yankewa hukuncin, wato Maryam Sanda ta hallaka mijinta Bilyaminu Bello.

A ranar 27 ga watan Janairun 2020 ne Mai Shari’a Yusuf Halilu ya yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya.

A ranar juma’a mai sharia Steven Adah, ya jagoranci alƙalai uku don yanke wannan hukunci. Adah ya ce kotun na da alhakin yin adalci kamar yadda doka ta tanada ba son zuciyarta ba.

Tags:
%d bloggers like this: