EndSARS: Gwamnatin Lagos ta Kalli Iyalen ‘Yan sandan da aka Kashe

  • Home
  • Labarai
  • EndSARS: Gwamnatin Lagos ta Kalli Iyalen ‘Yan sandan da aka Kashe

A ranar Alhamis ne gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwoolu, ya bada kyautar miliyan goma ga kowacce mata jami’an ‘yansanda da ta rasa mijinta zanga-zangar EndSARS.

Gwamna Sanwoolu ya cika alkawarin da ya dauka na sakawa ‘yan sandan da suka rasa rayukansu don ganin sun samar da zaman lafiya.

A ganwarsa da jami’an tsaro ya ce, “Wasu daga cikin jaruman yan sandanmu sun rasa rayukansu yayin kare mu lokacin zanga-zangar EndSARS,”

Ya kara da cewa. “Wadannan hafsoshi ne da aka tura kare iyalanmu daga yan baranda, amma aka kasha su a rikicin. A yau ina farin cikin sanar da rabon naira miliyan goma-goma ga kowanne cikin iyalan wadannan yan sanda.

 “Gwamnatin jiha za ta dauki nauyin karatun yaransu har su kammala jami’a.”

Tags:
%d bloggers like this: