“Dauko kwararru daga ketare ya fi karfinmu” In ji rundunar sojojin Najeriya

  • Home
  • Labarai
  • “Dauko kwararru daga ketare ya fi karfinmu” In ji rundunar sojojin Najeriya

Tun daga kisan wulakanci da aka yi wa wasu manoma a jihar Kano, wasu da suka yi fice a wajen tattauna matsalar tsaro, ke neman gwamnati ta dauko sojojin haya, da ake da su a kasashen duniya da kan kawo dauki, inda za a basu kwangila na abin da ake so su yi.

Sai dai rundunar sojojin Najeriya ta ce wannan bukata ta shallake ikonta. Wanda ya yi magana a kan wannan bukata a madadin rundunar tsaro, Janar John Enenche ya ce gwamnatin tarayya ce kadai ke da ikon dauko wasu sojoji daga ketare domin su taimaka wa Najeriya wajen yakar ‘yan ta’adda.

Ya ce “Iyayen gidanmu da su ka daukemu sun ce aiki ya yi mana yawa, ya rage nasu. Ba aikin soji ba ne su ce aiki ya yi masu yawa; Ni aiki bai yi mani yawa ba.”

“Idan na ce haka, ina nufin bana son in yi aiki. Kuma idan na ce ba haka ba ne, ina nufin ba a amfani da karfina kenan.” inji Janar John da yake magana a madadin gidan sojan.

Ya kara da cewa: “Maganar dauko kwararru daga ketare ta fi karfinmu. Irin dakarun da ake da su ya danganta ne da mutane, wannan ya zarce karfin ikonmu.”

Wannan magana ta dauko sojoji ta yamutsa hazo sosai a wannan sati. Hakan ya sa wani kwararre a kan harkokin tsaro Barista Bulama Bukarti da yake karatun digirinsa na uku a London, ya nuna rashin amincewarsa da wannan bukata.

A wata hira da Channels TV ta yi da shi, Bulama na ganin sojojin Najeriya za su iya yin wannan aiki matukar an basu kayan aiki da taimakon da ya kamata. Ya kuma nuna illar dauko sojoji haya, wanda sukan karya dokokin kasa da na duniya wajen aiwatar da aikinsu.

Tags:
%d bloggers like this: