TSAGIN BOKO HARAM NA SHEKAU SUN DAUKI ALHAKIN KISAN MANOMA 43

  • Home
  • Labarai
  • TSAGIN BOKO HARAM NA SHEKAU SUN DAUKI ALHAKIN KISAN MANOMA 43

Kungiyar Boko Haram tsagin Abubakar Shekau ta dauki alhakin kisan manoman Zabarmari 43 da aka yi a ranar Asabar.

Kungiyar ta amsa wannan laifi kisan manoma 43 a Zabarmari dake karamar hukumar Jere ta jihar Bornon Najeriya.

Hakan ya fito ta wani sabon faifan bidiyo da kungiyar ta fitar, inda ta ce harin da suka kai na ramuwar gayya ne, saboda kisan da sojojin Najeriya suka yi wa wasu ‘yan kungiyarsu.

Kungiyar ta gargadi jama’a kan liken asiri da suka ce ana yi musu tare da taimakawa jami’an tsaro.

Tags:
%d bloggers like this: