Kotu ta sallami Naziru Sarkin Waƙa

Wata kotun magistire dake garin Kano ta sallami Nazir Sarkin Waƙa bisa shariah da suke da gwamnatin jihar Kano. Kotun ta sallami Nazirun ne bayan takardar neman afuwa da ya turo ta hannun lauyansa.

Hukumar tace fina-finai ce ta jihar ta kama shi da laifin fidda wata waƙa ba tare da an tace ta ba.

A baya an kama Nazirun, wanda aka maka shi a kotu. Sai dai an bada shi a hannun beli bayan ya cika ƙa’ida. Amma a watan da ya gabata ne aka sake kama shi, wanda har sai da ya kwana a gidan maza.

Mutane da yawa musamman ‘yan fim na zargin gwamnatin Kano da amfani da hukumar wajen gallazawa wasu da ba su haɗa hanya ɗaya ba a siyasance.

Tags:
%d bloggers like this: