An Kama Abdulrasheed Maina A Nijar

Rahotanni na nuna jami’an tattara bayanan sirri sun kama Abdulrasheed Maina a daren ranar Litinin.

Kafar yada labarai ta BBC Hausa ta ruwaito cewa wani babban jami’in tattara bayanan sirri ya shaidawa ‘yan jarida cewa an samu nasarar kama Maina ne sakamakon irin dankon zumunci da kuma yarjejeniyar tsaro dake tsakanin Najeriya da Nijar.

Shi dai Maina wanda yake tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho na Najeriya garambawul na fuskantar shariah a Najeriya kan tuhume-tuhume 12, wanda hukumar EFCC ta shigar da shi kara.

A baya kotu ta bada shi beli, ta hannun Sanata Ali Ndume da ya tsaya masa. Sai dai a lokacin da kotun ke nemansa, sai ya yi batan dabo aka neme shi sama ko kasa aka rasa. Hakan ya sa kotu da bada umarnin kama wanda ya tsaya masa, wanda sai da kyar da jibin goshi aka bada belinsa.

%d bloggers like this: