Kasar Saudiyya ta yi tir da kisan da aka yi wa manoma a Najeriya

Kasar Saudiyya ta bi sahun dubban mutane masu amfani da kafofin sadarwa na zumunta, wajen yin Allah-wadai da kisan da aka yi wasu manoman shinkafa a jihar Borno.

Kasar ta Saudiyya ta sanar da wannan sako ta shafinta na Twitter, inda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce wannan abin takaici ne yadda mahara ke kai wa fararen hula hare-hare.

Sanarwar  ta ce, “Muna isar da ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda aka kashe da gwamnati da kuma daukacin mutanen Najeriya.

https://t.co/wQ20kitwRl?amp=1
Tags:
%d bloggers like this: