An yi jana’izar mutane 43 da ‘yan ta’adda suka kashe a Borno

  • Home
  • Labarai
  • An yi jana’izar mutane 43 da ‘yan ta’adda suka kashe a Borno

A ranar Lahadi aka gudanar da jana’izar mutane 43 da ‘yan ta’adda suka kashe a jihar Borno, a lokacin da suke aiki a gonar shinkafa.


Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya jagoranci ma’aikatan gwamnati da sojoji zuwa gurin jana’izar.
A ranar Asabar ne ‘yan ta’addan suka kai hari ƙauyen Zabarmari dake cikin Jere, a jihar Borno suka far ma manoman dake aiki a gonar shinkafar.

Wani Liman da ‘yan jarida suka tattauna da shi ya ce. “Manoma 60 aka yi jinga da su don girbe gonar shinkafar. Guda 43 an yi musu yankan rago, 6 sun ji raunuka.”

Tags:
%d bloggers like this: