Kungiyar Kwallon Kafa Ta Napoli Za Ta Maida Sunan Filinta Da Suna Maradona

  • Home
  • Wasanni
  • Kungiyar Kwallon Kafa Ta Napoli Za Ta Maida Sunan Filinta Da Suna Maradona

Biyo bayan mutuwar shahararren da wasan kwallon kafa a duniya, Diego Maradona a jiya Laraba, tsohowar kungiyarsa ta kwallon kafa, Napoli dake kasar Italiya ta yanke hukuncin sauya sunan filin wasanta daga San Paulo zuwa Maradona.

Kungiyar Napoli ta yanke wannan hukunci ne saboda gudunmawar da Maradona ya ba ta a lokacin da yake taka leda a kugiyar. Maradona ya bugawa Napoli wasa daga shekarar 1984 zuwa 1991, inda ya buga musu wasanni 188 ya sami nasarara jefa kwallaye 81.

Ta bangaren kofuna, Maradona ya lashe kofuna guda 5 tare da Napoli da suka haɗar da gasar Serie A guda 2 da gasar UEFA Cup guda 1 da gasar Supercoppa Italina guda 1 da kuma gasar Coppa Italia guda 1.

Wannan mataki da Napoli ta dauka ya zo ne a lokacin da shahararru a harkar kwallon kafa ke kokawa da mutuwar ta Maradona. Ko tsohon dan wasan Brazil Pele da ake alakanta kwarewarsa da ta Maradona, ya koka a jiya inda ya ce ya yi rashin dan uwa.

Tags:
%d bloggers like this: