“Babban abin da ya damu shugaban ƙasa shi ne ƙuri’armu” -Ƙungiyar Dattawan Arewa

  • Home
  • Labarai
  • “Babban abin da ya damu shugaban ƙasa shi ne ƙuri’armu” -Ƙungiyar Dattawan Arewa

Ƙungiyar Dattijan Arewa (NEF) ta nuna ɓacin ranta a kan Shugaban ƙasa Muhammad Buhari, musamman yadda ya gaza fitar da yankin arewa kunya, duk da irin koma baya da ƙalubale da yankin yake fuskanta ta ɓangarori da dama.

Jaridar The Guardian ce ta wallafa wannan labari a ranar Litinin 23 ga watan Nuwamba, inda ƙungiyar ta zargi gwamnatin Buhari da yin halin ko in kula da yankin na Arewa, wanda ya bada ɗinbin gudunmawa ga nasarar zaɓensa.

Tun bayan ziyarar aiki da minista Babatunde Fashola da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari suka kai, na ganin yadda aikin gyaran babban titin da ya tashi daga Kano zuwa Abuja ke tafiya, kafofin yaɗa labarai sun kawo rahoton kalamin ministan a kan cewa aikin ba zai gamu a zamanin gwamnatin Buhari ba, domin zai ɗauki tsawon shekara biyar kafin a gama, wanda hakan ya jawo ɓacin ran mutane da dama, musamman daga Arewa.

Wannan dalili ne ya sa ƙungiyar Dattawan Arewa ta magantu, ta hannun kakakinta, Hakeem Baba-Ahmed, wanda ya zargi gwamnatin Buhari da yi wa aikin titin riƙon sakainar kashi, musamman idan an yi la’akari da mihimmancin titin ga mutanen Arewa.

Kungiyar Dattijan Arewa ta koka yadda tun a shekarar 2017 aka bada kwangilar aikin titin, amma ba a fara aikin ba sai a shekarar 2018.

A cewar ƙungiyar, yadda aikin babbar hanyar ke tafiyar hawainiya, ya nuna a fili shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bai damu da matsalolin da suka addabi yankin na Arewa ba.

Ƙungiyar ta ce; “babban abin da ya damu shugaban ƙasa shi ne ƙuri’armu.”

Ita ma takwararta, Ƙungiyar tuntuba ta arewa (ACF) ta aika saƙo makamancin wannan zuwa ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, kamar yadda jaridar The Cable ta rawaito.

Tags:
%d bloggers like this: