Rashin ɗaukar shawara ne ya jefa Najeriya cikin karayar tattalin arziƙi-Atiki Abukakar

  • Home
  • Labarai
  • Rashin ɗaukar shawara ne ya jefa Najeriya cikin karayar tattalin arziƙi-Atiki Abukakar

Atiku Abubakar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyar PDP ya nuna rashin jin daɗi da halin da Najeriya ta tsinci kanta na karayar tattalin arziƙi.

A cewarsa inda gwamnati ta yi aiki da shawarwari da ya bayar da waɗanda masana ke bayarwa, da Najeriya ba ta tsinci Talatarta a Laraba.

Atikun wanda yake tsohon shugaban ƙasa ne, kuma babban ɗan kasuwa ya yi wannan furuci a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya yi dogon sharhi tare da kawo tsare-tsare da hanyoyi da gwamnati ya kamata ta yi amfani da su wajen fita daga wannan hali. Daga ciki ya ce dole ne Najeriya ta rage kuɗin da take kashewa gurin gudanar da mulki, da kuma tattalin kuɗaɗe da take da shi tare da gudun ciwo bashi.

Atiku ya kawo irin abubuwan da ya kamata a ƙarawa haraji, amma ya ce rashin imani a ƙarawa talakawa kuɗin abinci yayin da abubuwa na more rayuwa ba a ƙara musu kuɗi ba.

Tags:
%d bloggers like this: