Najeriya ta sake faɗawa cikin karayar tattalin arziƙi

  • Home
  • Labarai
  • Najeriya ta sake faɗawa cikin karayar tattalin arziƙi

Wasu alƙaluma da Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya ta fitar ranar Asabar, ya nuna ƙasar ta sake faɗawa mashasshara ko karayar tattalin arziƙi.

Domin alƙaluma da National Bureau of Statistics suka fitar sun nuna tattalin arziƙin Najeriya ya ragu da kashi 3.62 cikin 100 a tsakanin watan Yuli zuwa Satumban 2020.

Wannan matsalar karayar tattalin arziƙi ta zo wa Najeriya a lokacin da take ƙoƙarin fita daga tarun matsaloli da cutar korona ta kawo wa ƙasar.

Farashin kayan abinci ya tashi, ma’aikatu da masana’antu sun rage ma’aikata tare da yawan adadin abin da suke sarrafawa. A dai cikin wannan lokaci na korona darajar naira a ƙasar ta faɗi sosai, wanda haka ya taimaka wajen hauhawar farashi.

Wannan yanayi zai sa gwamnati ta sake waiwaiyar yadda take gudanar da wasu ayyuka, musamman don ganin an rage kaifin abin da wannan matsala za ta haifar.

Tags:
%d bloggers like this: